Blog
Yadda Ake Samun Web3 Jobs [Secrets You Need to Know]
- May 28, 2025
- Posted by: Joseph Micheal
- Category: Cryptocurrency
![Yadda Ake Samun Web3 Jobs [Secrets You Need To Know] Yadda Ake Samun Web3 Jobs](https://simasacademy.com.ng/wp-content/uploads/2025/05/Yadda-Ake-Samun-Web3-Jobs-1170x500.webp)
Web3 jobs na nufin kowanne irin aiki da ke da alaka da fasahar Web3, musamman wadanda ke cikin decentralized ecosystem kamar aikin smart contract developer, community manager, content creator, UI/UX designer, crypto researcher, da sauransu. Wadannan ayyukan ba dole sai ka kware wajen programming ko coding bane zaka iya yi. Da akwai ayyuka da dama da kowa zai iya farawa idan yana da ilimi da kuma kwazo a bangaren.
Mecece Web3?
Web3 wata sabuwar fasahar Intanet ce da ke bada dama ga mutane su mallaki bayanansu da dukiyoyinsu kai tsaye ba tare da tsoma bakin manyan kamfanoni ba. Wannan tsarin yana amfani da blockchain, cryptocurrency, da kuma decentralized platforms wajen canza yadda ake amfani da Intanet gabadaya. Daga cikin manyan bangarorin da Web3 ke tasiri akwai DeFi (Decentralized Finance), NFTs, DAO, da kuma Metaverse.
Web3 na bada dama mai yawa ga matasa musamman ‘yan Afrika wajen samun ayyuka da kudaden shiga ta hanyar kwarewa da ilimin zamani.
Matakan Da Zaka Bi Ka Samu Aikin Web3
Wadannan sune matakan da zaka bi su daki-daki domin samun dacewa a harkar web3 jobs Insha Allah;
- Ka Fahimci Menene Web3 – Ka ringa bincike sosai kan blockchain, crypto, NFTs, DAOs da sauran fasahohin Web3.
- Ka Zabi Inda Kafi Kwarewa – Ka zabi shashi ko fannin da yafi maka (misali: content creation, graphics design, developer, moderator, VA, da sauransu).
- Ka Koyi Skill Din – Zaka iya amfani da online courses da zasu koya da kai (kamar na Simas Academy ko Flowdiary) cikin harshen Hausa.
- Ka Gina Portfolio – Ka gwada yin wasu ayyuka na gwaji (sample works), ko ka shiga aiki a volunteer projects domin ka tara portfolio.
- Shiga Web3 Communities – Kasance cikin Discord servers, Telegram groups da Twitter spaces na Web3 domin samun sabbin updates ko sanarwa, kamar kana gina connection ne.
- Application Da CV – Ka tanadi CV dinka wanda ya dace da remote/Web3 jobs, duk lokacin da ake bukatar wani role kai tsaye sai ka aika.
- Personal Branding – Ka gina social media dinka musamman Twitter/LinkedIn don bayyana kanka da irin abinda kake yi. Ka gujewa posting na shirme, ka gujewa posting na banza, saboda social media shine CV dinka.
- Ka Kasance Mai Hakuri Da Juriya – Ba’a samun kowane irin aiki cikin sauki, ballentana kuma web3 jobs da suke da wahalar sha’ani, dole kana bukatar hakuri sossai kafin kayi nasara a wannan fannin.
- Kar Ka Daina Neman Skills – Sabbin abubuwa suna fitowa kullum a Web3, ka kasance mai kula da abubuwan kana kara iliminka.
Dalilan Da Yasa Web3 Jobs Suke Da Mahimmanci
- Ana Biya Da Cryptocurrency – Idan kayi aiki to za’a biya ka ne da kudade kamar USDT, USDC, ETH, da BTC ko SOL, wanda ke da saukin canzawa zuwa naira. Kuma idan ka sauya zaka gansu da auki sossai.
- Remote Ne – Ayyukan Web3 ba sa bukatar sai ka mallaki office ko wajen aiki na musamman. Za ka iya yin su daga gida kuma ko daga ina kake.
- Ana Kara Bukatar Kwararru – Yayin da Web3 ke kara yaduwa a duniya, kungiyoyi da dama na bukatar ma’aikata masu basira da sabbin strategies.
Ire-Iren Ayyukan Da Zaka Iya Yi A Web3
Wadannan wasu ne daga cikin ayyukan da zaka iya yi a lokacin da kake neman Web3 Jobs;
Community Manager
Community manager shine ke jagorantar mutane a social platforms irinsu Discord, Telegram, Reddit, da Twitter. Ayyukansa sun hada da amsa tambayoyi, shirya taro, da samarwa community nutsuwa kan project. Kana bukatar strong communication skills da fahimta game da project din kafin ka fara.
Content Creator/Writer
Wannan shine mai rubuta blog posts, social media threads, newsletters ko technical documents da ke bayani akan project din. Zai iya aiki da marketing ko education team. zaka iya samun aiki idan kana da kwarewar SEO, research, da storytelling.
Graphics Designer (NFT Art)
Idan ka zama Graphic designer a web3 zaka ringa zane-zane domin samar da NFT collections, branding, UI/UX, da sauran abubuwan da mutane suke kallo. Zakayi aiki da illustrators da art directors. Ana amfani da software irin su Adobe Illustrator, Photoshop, ko Figma da sauransu.
Discord Moderator
Discord mod shi ke kula da zirga-zirga da bin ka’ida a Discord server na project. Yana hana spam, yana amsa tambayoyi, da taimakawa sabbin shiga. Ana bukatar presence, patience, da knowledge of community rules.
Translator (Hausa to English, Or English To Hausa)
Web3 projects na duniya suna bukatar wadanda zasu fassara musu bayanai zuwa harsuna da yawa, musamman wajen onboarding new users daga Africa, Asia, da sauransu.
Social Media Manager
Aikin SMM shine kula da shafukan social media na project din wajen posting din contents, engaging da followers, da planning strategy. Kana bukatar ilimin social media marketing skill kafin ka tinkari wannan. Muna da wannan course din a Simas Academy, zaka iya zuwa ka karanta kuma ka samu Certificate.
Virtual Assistant (VA)
VA wato Virtual Assistant shine yake taimakawa da kananan ayyuka kamar scheduling, email handling, da basic research. Web3 startups suna yawan bukatar VA. Ana bukatar mutum mai organization da responsiveness.
Crypto Researcher or Analyst
Wannan mutumin shi ke nazarin projects, blockchain tokens, trends, da competition. Suna rubuta reports ko gabatar da findings.
Frontend/Backend Developer (Web3 tools like Solidity)
Developers su ke gina decentralized apps (dApps), smart contracts, da wallet integration. Kana bukatar sanin Solidity, Rust, JavaScript, React, Node.js, da Web3.js. Wannan na ɗaya daga cikin manyan high-paying jobs a Web3 Jobs.
Abubuwan Da Zaka Kula Da Su
- Kar Ka Saka Kudi: Legit Web3 jobs ba su da registration fee. Idan akayi maka maganar kudi to da akwai yiwuwar scam ne. Sai dai idan wanda zai maka hanya ne zai bukaci wani abu (akwai yiwuwar hakan).
- Ka Tabbatar Da Ingancin Project Din Da Kake Shiga: Wasu projects din scam ne. Dole kayi bincike a kansu kafin ka karbi aikinsu saboda zaka iya kasancewa cikin wadanda za’a kama idan asirinku ya tonu.
- Ka Kula Da Lokaci Da Deadlines: Aiki a Web3 yana bukatar ayi shi a kan lokaci, basu wasa da deadlines.
- Ka Zama Ankararre: Ka kula da wallet, seed phrase da password dinka sosai kar a garin neman kiba a samo rama.
Shawara Daga Aliyu Saidu Jauro
![Yadda Ake Samun Web3 Jobs [Secrets You Need To Know] Yadda Ake Samun Web3 Jobs](https://simasacademy.com.ng/wp-content/uploads/2025/05/Yadda-Ake-Samun-Web3-Jobs-1024x559.webp)
Samun aiki a Web3 ba abu ne mai sauki ba. Aikin yana bukatar sadaukarwa, koyon sabbin abubuwa, da kuma jajircewa sosai. Yana ɗaukar lokaci, yana bukatar hakuri, kuma zaka fuskanci kalubale da yawa kafin ka fara ganin sakamako.
Amma fa, idan ka dage, ka koya skill, ka shiga community, ka yi aikace-aikace koda kyauta ne a farko to wallahi, zaka iya bude wata sabuwar kofa a rayuwarka. Web3 na biyan ma’aikata sosai idan har ka cancanta. Za ka iya samun aiki daga nan gida (remote) Nigeria, kana samun kudinka kuma kana sake kara ilimi da connection (Saboda gaba kaine zakayiwa mutane hanya).
Ka kwantar da hankalinka, kada ka dubi yadda ka dade kana ganin baka da sa’a. Idan wasu sun iya, kai ma zaka iya. Kawai ka fara da abu daya: Ka fara yanzu. Ko da joining group daya ne, ko karanta article daya ne, a hankali a hankali zaka ga sauyi.
Ina fatan ka dauki wannan shawara, kuma karka manta babu mai hanaka sai dai idan kai ka hana kanka.
Menene Ma’anar Web3 Jobs?
Web3 jobs na nufin ayyuka da suka danganci sabon tsarin yanar gizo wanda ke amfani da blockchain da cryptocurrency. Ayyukan nan ba wai coding kadai ba ne, akwai dama ga masu kirkira, masu tsara al’umma, da masu fassara.
Shin Zan Iya Samun Aikin Web3 Ko Da Ban Iya Coding Ba?
Eh zaka iya. Akwai ayyuka da dama kamar Community Manager, Video Editor, Social Media Manager da dai sauransu da basa bukatar coding.
Ta Ina Zan Fara Hada Kaina Da Web3 Opportunities?
Fara da koya ilimi game da crypto da Web3, ka shiga communities kamar Discord, Telegram, da Twitter. Kana iya amfani da Gitcoin ko Bounties domin fara da kananan ayyuka.
Shin Da Gaske Ana Biyan Ma’aikata A Web3?
Eh, amma sai ka nuna kwarewa da dagewa. Ana biyan ta crypto ko stablecoins, kuma yawanci ba a bukatar degree.
Wane Iri Na CV Nake Bukata Domin Neman Web3 Job?
CV dinka ya kamata ya bayyana kwarewarka, portfolio, links zuwa GitHub, blog, ko duk inda kake nuna aikinka. Ka rinka amfani da profile kamar Notion ko LinkedIn.
Shin Akwai Yuwuwar Inyi Aikin Remote Ne Kawai?
Yawancin Web3 jobs remote ne wato online. Wannan yana nufin zaka iya aiki daga gida ko duk inda kake muddin kana da internet mai kyau.
Shin Akwai Wuraren Da Zasu Taimaka Min Nemi Aiki?
Tabbas da akwai communities kamar Web3Bridge, Bankless DAO, da Developer DAO, Simas Jobs, inda ake taimaka wa matasa su samu aiki, mentorship, da network.
Ina Zan Koya Abubuwan Da Nake Bukata?
Zaka iya koyo daga Simas Academy, inda muke da courses kan digital marketing, video editing, da content creation, duka suna da amfani a duniyar Web3.
Shin Akwai Hatsari A Cikin Web3 Jobs?
Kamar kowanne aikin yanar gizo, akwai scammers. Ka guji bawa wani private key, kuma ka tabbatar da platform din da kake aiki dashi.
Yaya Zan Gina Kaina A Web3?
Ka fara da aiki kyauta a kan wasu projects domin gina reputation. Ka ringa posting na abinda kake yi a X (Twitter), LinkedIn, da kuma shiga tattaunawa a Discord.