Blog
Makarantu 5 Da Zaka Koyi Ilimin Computer & Internet Da Hausa
- June 15, 2025
- Posted by: Joseph Micheal
- Category: Hausa

Kanason Koyon ilimin Computer? Yakamata. Domin A wannan zamani na fasaha, ilimin Computer ya zama kamar wajibi ne ga duk wanda ke son rayuwa mai inganci. Koda kai Dalibi ne, Dan kasuwa, ko kuma mai neman aiki (Musamman a kasashen Turai ko Larabawa), sanin yadda ake amfani da Computer, internet, da sauran kayan aikin zamani yana da matukar amfani. Abin farin cikin shine, yanzu akwai makarantu da yawa da ke koyar da ilimin computer da harshen Hausa, ta hanyar online ko a zahiri, kuma suna da darussa masu amfani da za ka iya fara koyo nan take bayan ka shiga.
A wannan rubutun, mun binciko makarantu 5 da suka shahara wajen koyar da ilimin Computer da harshen Hausa, tare da cikakken bayani game da su, abubuwan da suke koyarwa, hanyoyin karantarwar, da dalilin da yasa ya kamata ka shiga kowanne. Ka tabbata ka karanta har karshe domin ka gano wacce makaranta ce ta fi dacewa da kai.
Simas Academy
Ta Farko, Simas Academy, tana daya daga cikin manyan makarantun dake koyar da ilimin computer da harshen Hausa a duniya. Makarantar tana bayar da ilimi na zamani ta hanyar online da physical training, inda take da ofisoshi a Yola da Kano.
Abubuwan Da Ake Koya A Simas Academy:
- Basic & Advanced Computer Skills
- Blogging & YouTube (da Hausa)
- Kasuwanci
- Video Editing, Graphics Design
- Internet Marketing
- AdSense, AdsTerra, Monetag Monetization
- 3D/2D Animation
- Social Media Marketing
- Affiliate Marketing, Personal Branding
- Rubutu (Copywriting, SEO Blogging)
Babban abin burgewa shine ba iya Hausa suke koyarwa ba, Simas Academy tana Koyar da ilimin computer/internet da Turanci da Kuma Hausa. Haka zakalika, bayan ka kammala karatu zaka samu takardan shaidar kammalawa (certificate), mentorship kai tsaye, affiliate program, da kuma tsarin samun kyaututtuka.
Flowdiary

Na Biyu, Flowdiary, wanda wani matashi (Muhammad Mohidden) ya kirkiro. Makaranta ce da ke bayar da horo na digital skills da harshen Hausa, musamman ga matasa masu sha’awar kirkiro da sabbin abubuwa. Asalin makarantar na da office a Yobe State, amma tana aiki gaba daya a yanar gizo. An kafa Flowdiary ne domin magance matsalar da matasa ke fuskanta wajen samun ilimi da sana’o’i na zamani.
Courses Na Flowdiary Sun Hada Da:
- Full Stack Web Development
- Android App Development
- Bug Bounty
- Ethical Hacking
- Graphics Design & Video Editing
- Forex Trading & Cryptocurrency
- UX/UI Design
- Social Media Management
Abin sha’awa a Flowdiary shine suna da mobile app da yake da saukin amfani, inda daliban Flowdiary suke karatu, da kuma tests domin tabbatar da fahimtar mutum. Suna da certificates da ake iya amfani da su wajen neman aiki, da kuma scholarships da creative hall awards don daliban da suka fi kokari.
Flowdiary ya samu yabo daga duniya, inda suka kasance daga cikin masu wakilcin Nigerian Startups a GITEX Africa 2025, kuma sun shiga Northeast Innovation Challenge, kuma sun lashe. Haka kuma suna gudanar da taruka na kai tsaye, coaching, mentorship, da hanyoyin hada kai da manyan kamfanoni.
Bitkova Digital Hub

Bitkova Digital Hub (Makarantar mu abin alfaharin mu) wata babbar makaranta ce da ke Gombe, Nigeria, wadda take mayar da hankali wajen koya wa matasa da ‘yan kasuwa ilimi akan crypto, web3, da digital marketing. Wannan makaranta tana taka muhimmiyar rawa wajen horar da manyan kwararru a Arewa. Misali irinsu Sanusi Danjuma Ali, Da Sauransu.
Abubuwan da ake Koya Daga Bitkova
- Certified Cryptocurrency Market Analyst
- Blockchain Development (Solidity, Smart Contracts)
- UI/UX Design
- Crypto Trading & Risk Management
- Digital Marketing
Bitkova sun fi gudanar da live classes, sa’annan suna bayr da takardar shaidar kammalawa, da kuma intership/ayuka ga daliban da suka gama. Har ila yau, suna da shahararren “40-day Solidity Challenge” wanda aka gabatar da shi da harshen Hausa, daya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin matasa a Arewa.
Malamiromba
Malamiromba Ltd, wata cibiya ce da take da asali daga Kano wadda ta tsunduma cikin career development, Musamman ta hanyar amfani da AI.
Cikin Abubuwan Da Malamiromba Ke Koyarwa Akwai:
- UI/UX Design
- Web Development
- Digital Marketing
- CV/Resume Building
- Data Analysis
- Career Coaching
- Remote Job Training
Malamiromba na da malamai da yawa daga bangarori Daban-Daban da suka mayar da hankali wajen koyar da dalibansu. Kuma kamar kowacce makaranta Malamiromba suna bada Certificate ga daliban da suka kammala karatu.
Hausa Academy
Hausa Academy wani makaranta ne da ya kware wajen koyar da Cybersecurity, Networking, Programming, da Computer Basics gaba daya da harshen Hausa. Wannan yana taimaka wa matasa da tsofaffi su fahimci abubuwan da ke da wahala idan da Turanci aka koya musu su.
Darussan Da Hausa Academy Suke Koyarwa:
- Cybersecurity Course
- Ethical Hacking & Penetration Testing
- Computer Networking
- Programming Languages (Python, C++, Java)
- Operating Systems
- Networking, Da Sauransu
Hausa Academy na bayar da takardun shaidar kammala karatu, kuma suna da free courses da paid courses. Suna da live classes, group discussions, WhatsApp, da Hausa. Wannan makaranta ta dace da kowa da kowa musamman masu sha’awar cybersecurity da programming, domin yana koyar da lamarin cikin sauki.
Wacce Makaranta Ce Ta Dace?
Dukkanin wadannan Makarantu ko kuma muce Platforms guda biyar suna da inda suka fi karfi wato bangarorin da suka fi kwarewa. Saboda haka ya danganta da abinda kake da bukata:
Simas Academy – Idan kana son koyon ilimin Kasuwanci, Content Creation, Digital Marketing, da Monetization cikin harshen Hausa.
Flowdiary – Idan kai matashi ne mai sha’awar development ko kana so ka Kirkiro wani abu sabo na musamman.
Bitkova – Idan kana son shiga Harkar crypto, blockchain da web3, ko kuma kowane kalar Trading sai kazo nan.
Malamiromba – Idan burinka shine aikin yi kai tsaye, ko kuma fara Career dinka da neman aiki a online ko Amfani da AI Wajen dogaro da kai.
Hausa Academy – Idan kana da niyyar zama cybersecurity expert ko programmer zaka iya koya da Hausa.
FAQs
Wace Makaranta Ce Ta Fi Dacewa Ga Sabbin Masu Koyo?
Simas Academy, Saboda A Cikin Courses Ɗinsu Har Na Yara Akwai. Ga Sabbin Shiga Suna Iya Samun Beginners Course Inda Akayi Bayanin Komai A Saukake.
Bayan Na Kammala Karatu Zan Samu Certificate?
Eh, Dukkan Makarantun Suna Bayar Da Certificate Bayan Kammala Koyon Kowane Course, Musamman Simas Academy, Flowdiary, Da Bitkova.
Idn Inason Zama Hacker, Wace Makaranta Ce Tafi Dacewa Dani?
Idan Kana Son Koyon Hacking (Ethical Hacking) To Tabbas Hausa Academy Tafi Dacewa Da Kai.
Idan Inason Zama Programmer, Na Ringa Kirkiro Da Abubuwa Ina Zanje?
Flowdiary, Domin A Flowdiary Sunfi Mayar Da Hankali Wajen Koyar Da Skills Da Zasu Taimakawa Mutum Ya Gina Skills Ɗinsa Bangaren Development.
Idan Inason Koyon Samun Kudi Nan Take Wace Makaranta Ce Tafi Dacewa?
Babu. A Cikin Waɗannan Makarantu Gabadaya Basu Koyar Da Abinda Zaka Zo Nan Take Ka Samu Kudi. Ilimi Ake Bayarwa, Wanda Idan Ka Tsaya Ka Koya Kuma Kayi Aiki Dashi Ba Zaka San Lokacin Da Kudi Zasu Fara Zuwa Maka Ba.
A Ina Zan Koyi Ilimin Kasuwanci?
Idan Ilimin Kasuwanci Kakeso Da Kuma Hanyoyin Da Zaka Iya Juya Kudadenka A Internet, To Tabbas Simas Academy Tana Koyar Da Wadannan.
Wanne Yafi Dacewa Da Masu Sha’awar Sana’ar Crypto?
Bitkova Digital Hub Shi Yafi Dacewa Ga Masu Sha’awar Crypto, Blockchain Da Trading.