Idan kana social media kuma baka bibiyan wadannan mutanen to sai dai muce maka Innanillahi. A wannan zamanin da social media ta zama abokiyar rayuwa, da akwai wadanda suke bayar da ilimi a cikinta, kuma kyauta. Kawai bibiyarsu zakayi amma duk lokacin da suka wallafa sabon ilimi zaka kalla. Wadannan Hausawa ne, da suka sadaukar da lokacinsu domin mu gabadaya, kuma suna bada ilimin da ko Jami’a ba lallai ka samu ba. Shiyasa Simas Academy ta hada bayanansu ta kawo muku 15 Hausa Influencers Da Ake Samun Ilimi Daga Garesu a Facebook. Karka tsaya jira muje zuwa.
Wannan ya samo asali ne daga kuri’ar da Simas Academy ta gudanar a Facebook, inda kowa ya zabi gwaninsa. Karku manta kowane Influencer da bangaren da yafi mayar da hankali a kai.
Jerin Hausa Influencers Da Zaka Samu Ilimi A Wajensu
15. Amina Ibrahim Idris
Amina Ibrahim Idris (Entrepreneur) ta shahara wajen koyar da matasa da kuma life coaching. Hajiyar wacce ta kasance yar Kano tana amfani da Facebook wajen bada shawari, kawo contents da cigaba da kuma wasu lokutan tana son wallafa barkwanci. Bugu da kari, Amina tana bada mentorship musamman ga mata bangaren Fasaha.
Facebook: Amina Ibrahim Idris, X: Amina Idris.
14. Salisu Abdurrazak Saheel
Dr. Salisu Abdurrazak Saheel kwararre a fannin cybersecurity da fasahar zamani, marubuci, kuma yana aiki da Jami’ar Ado Bayero University dake Kano. Yana koyar da tsaro na zamani a shafinsa, inda yake bada shawarwari kan yadda za’a tsare bayanai da kuma dukiya a internet. Salisu yana da digiri a fannin fasaha da bincike kan hanyoyin kare bayanai daga hare-haren yanar gizo. Shi ne mai kamfanin ArtificialX Technology LTD, da kuma SalFat Data. Madalla da Dr. Saheel dan gidan Professor (Sheikh Isah Ali Pantami).
Facebook: Salisu Abdurrazak Saheel.
13. Babangida Ruma
Dr. Babangida Kabir Ruma masanin harkokin yau da kullum ne, musamman bangaren Fasaha da samar da ayyuka a Nigeria. Dan kasuwar zamani da yake samar da cigaba ta hanyoyin dake taimakawa matasa su samu damar ayyuka da karin ilimi a fannin fasaha. Babangida Ruma, yana daga cikin wadanda suka taka rawa wajen samar da Fasahar zamani a Ruma, Katsina, dama Duniya baki daya.
Shine ya samar da gidauniyar Ruma Foundation, domin taimakawa al’ummarsa. Shima yana son barkwanci, amma kasancewa dashi zai taimaka maka sossai wajen gina career dinka. Dama kuma wannan burinmu ne a Simas Academy, wato gina Career da kasuwanci.
Facebook: Babangida Ruma, X: Babangida Ruma LinkedIn: Babangida Ruma.
12. Abba Sani Pantami
Comr. Abba Sani Pantami (wato dan gwagwarmaya) dan jaridar zamani ne, marubuci, kuma masani kan sadarwa, wanda ya kirkiro Abba Pantami Data. Yana yada labarai kan al’amuran yau da kullum a shafinsa na Facebook, inda yake tattauna batutuwa kan siyasa, al’adu, da ilimi. Comarade, shine ya zo na 12 a sakamakon da muka samu.
Facebook: Abba Sani Pantami X: ComrAbbaSaniPantami.
11. Ahmad Aminu Ahmad
Ahmad Aminu Ahmad karantaccen lauya ne, wanda ke koyar da al’umma kan ilimin Fasaha da kuma Internet. Shi ne ya kafa Naija Kids Tech Learn, wanda ke koyar da yara fasahar zamani. Sa’annan shine ya samar Da kamfanin zamani na Hammad Technologies And Consultancy Ltd.
Ahmad, a koda yaushe yana amfani da iliminsa don taimakawa al’umma wajen koyar dasu abubuwa masu yawa, musamman a Facebook, hatta YouTube, ya kan dauki lokacinsa mai daraja ya kawo wani abu mai muhimmanci. Jazakallahu Khairan! Nima na tabbata ba zakuyi da na sanin kasancewa dashi ba.
Facebook: Ahmad Aminu Ahmad YouTube: Ahmad Aminu Ahmad.
10. Mahmoud Muh’d Sardauna
Mahmoud Muh’d Sardauna kwararre ne a bangaren blockchain da ilimin cryptocurrency, shugaban yan baiwa, wanda ya kafa makarantar zamani ta Bitkova Academy, wanda ke koyar da fasaha a harshen Hausa. A koda yaushe ya kan kawo sabbin dabaru da hanyoyin da yan baiwa zasu bi domin dogaro da kansu a yanar gizo. Mahmoud yayi aiki a wasu daga cikin kamfanonin fasaha na duniya, kuma a koda yaushe yana karfafa matasa su shiga duniyar digital da kasuwanci.
Facebook: Mahmod Muh’d Sardauna LinkedIn: Mahmoud Muhd Sardauna.
9. Aliyu M. Ahmad
Na tara a jerin shine, Aliyu M. Ahmad wanda ya kasance marubuci, manazarci, kuma kwararre a fannin design da fasahar zamani. Yana koyar da ilimin fasaha da ilimin rayuwa, inda yake bada shawarwari kan ginda manufa a rayuwa. Aliyu yana da degree a fannin computer science, kuma yana taimakawa da iliminsa ta bangarori da yawa a Facebook.
Facebook: Aliyu M. Ahmad Blog: Aliyu M. Ahmad
8. Muhammad Ubale Kiru
Dr. Muhammad Ubale Kiru ko kuma muce dashi international ya kware wajen tabo kowane bangare na rayuwa kuma ya bayyana ta ga al’umma. Makarancin computer ne, da yake da ilimin Fasaha da Internet, ba iya fasahar yake koyar ba hatta wasu bangarori na rayuwa, ya kan tabo batutuwa game dasu ya kuma bada shawari a kai. Idan kana Facebook karka bari ace baka tare da Dr. Muhammad.
Facebook: Muhammad Ubale Kiru X: Muhammad Ubale Kiru
7. MAHDY TECH
Na Bakwai, MAHDY TECH, wanda ya kasance dandali na musamman dake koyar da fasaha a harshen Hausa, Mahdi Ado Ibrahim, wanda ya kasance mamallakin Mahdy Tech ya jima yana wannan gwagwarmaya ta koyawa mutane ilimin Fasaha. Asalinsa dan Katsina ne, kuma ya kasance cikin jagorori a fannin tech education, kuma yana cikin jerin manyan influencers a Arewacin Nigeria.
Facebook: Mahdy Tech YouTube: Mahdy.
6. Dan Bello
Na shida, Bello Galadanchi, wanda aka fi sani da Dan Bello, shima zamu iya kiran sa da international, domin dan barkwancine, da yake da salon nishadantarwa, fadakarwa ta hanyoyi daban-daban, tsohon mai watsa labarai ne a Jaridar BBC da VOA. Yana zaune a China, inda yake yiwa kasar aiki, tare da gudanar da kasuwancinsa a nan Nigeria. Yana amfani da barkwanci wajen yada ilimi kan al’amuran yau da kullum ta hanyar bidiyoyinsa. Dan Bello yana da digiri na digirgir a ilimi, kuma yana da kyakkyawar goyon bayan al’umma, wannan ne masa yasa ya shigo cikin jerin. Muje Zuwa Dan Bello!
Facebook: Dan Bello Tiktok: Dan Bello Instagram: Dan Bello
5. Sanusi Danjuma Ali
Na shida a jerin shine, Sanusi Danjuma Ali wanda ya kasance jagora a duniyar Web3 da kasuwancin crypto a nahiyyar Africa gabadaya. Shine ya samar da kafar SCTvAfrica, wanda ke da al’umma fiye da 300,000. Ya kware wajen koyar da yadda za a yi amfani da fasahar blockchain domin samun kudi. Sanusi yana da kyakkyawar tarihi a fannin kasuwanci da fasaha, kuma ya kasance mai karfafawa matasa gwiwa su shiga duniyar internet. Nima shine gwanina, domin baya rowar ilimi a duk inda yake!
Facebook: Sanusi Danjuma Ali X: Sanusi Danjuma Ali
4. Yahaya Abubakar (Dogon Daji)
Na hudu a nan shine, Yahaya Abubakar, wanda aka fi sani da Dogon Daji, dan jaridar zamani da yake da kwarewa a barngaren Fasaha. Sa’annan a koda yaushe kasancewarsa a yanar gizo yana taimakawa mutane da ilimin al’amuran yau da kullum, kama daga ilimi har da shawari dangane da harkokin rayuwa.
Facebook: Yahaya Abubakar
Kafin Muje Ga Sauran Ukun, Ka Tabbata Kana Bibiyar Sauran Sha-Biyun.
3. Abdul-Hadee Isah Ibraheem
Gwanin mu shine ya zo na uku, wato Barr. Abdul-Hadee Isah Ibraheem wanda ya kasance kwararren kuma jagora a bangaren cryptocurrency. Sa’annan malami mai ilimin addini da samar da cigaba ga addini. Shima Barrister manazarci ne, dake yada ilimi kan fasaha da karawa yan uwa matasa kwarin gwiwa kan ilimin internet.
Ayyukansa basu tsaya iya nan ba, Barr. kamar shugaba yake, wanda ke samar da mafita, kawo sauyi mai kyau, da kuma taiamakawa wadanda suke bukata. Ya bada gudumawa da yawa ta bangarorin fasaha, ilimi da kuma addini.
Facebook: Abdul-Hadee Isah Ibraheem X: Abdul-Hadee Isah Ibraheem
2. Bashar Gulumbe
Na biyu daga cikin wannan jerin shine Dr. Bashar Haruna Gulumbe, lecturer ne a fannin ilmin halittu a Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, wato Federal University, Birnin Kebbi. Shi din kwararre ne wajen bincike kan kananun halittu. Shima ya taimaka, kuma har yanzu yana taimkawa wajen bada ilimi da contents masu ma’ana. Yana taimakawa mabiyansa wajen samun aiki, tallafin karatu wato scholarships, da ilimin AI a shafinsa na Facebook. Dr. yana da digiri na digirgir a ilmin halittu, kuma yana cikin kungiyar ‘Yan Jarida Masu Yaki da Superbugs a Afrika.
Facebook: Bashar Gulumbe X: Bashar Gulumbe.
Kafin Muje Ga na daya ka tabbata kana tare da Simas Academy a kowane platform, domin duk inda iliminka da karuwar yake nan muke.
1. Ibrahim Zubairu (Malamiromba)
Wanda yazo na farko shine, Ibrahim Zubairu, wanda aka fi sani da Malamiromba, jagorane a fannin fasaha da ilimi a harshen Hausa. Yana da ilimi da kwarewa a bangarori daban-daban na zamani, shima zamu iya kiransa da international. Shi ne ya samar da kafar Malamiromba Ltd., inda yake koyar da fasahar AI da karfafawa mutane gwiwa a duniyar fasaha. A koda yaushe burinsa shine samar da ilimin fasaha, kawo cigaba da kuma ganin an hada kai wajen cimma kyakkyawar manufa a Arewa baki daya.
Facebook: Ibrahim Zubairu – Malamiromba LinkedIn: Ibrahim Zubairu.
Sauran Wadanda Suka Bayyana A List Din
Bayan wadannan top 15 din da akwai kuma wasu fitattun influencers din da kuri’ar da suka samu bashida yawa. A ciki akwai Grema Yahaya Alhaji, Yakubu Sani Wudil, Jaafar Jaafar, Auwalu El-Yobawi, Halima Zakariyya, Sukairaj Hafiz Imam, Aliyu Saidu Jauro, Aliyu Tijani Aliyu, Muhammad Auwal Ahmad, Adam Muhammad Mukhtar, Mustapha Shehu da sauransu. Wadannan mutane sun kasance masu yada ilimi mai inganci a fannonin addini, fasaha, da kyawawan al’adu.
Darasin Da Zamu Dauka Game Da Wadannan Bayin Allah
Wadannan influencers din akoda yaushe suna nuna mana cewa duk yadda mukaso zamu iya yi da rayuwarmu; Idan muka ga dama zamu iya zama abinda muke son zama, ko samun abinda muke nema ta hanyar tashi tsaye mu nemi abin da gaske. Amma mafi muhimmanci, yin komai da ilimi shine kan gaba, sa’annan mu hada da hakuri, da sanyawa ranmu cewa zamu samu, amma ba da sauki ba.
Dole mu fuskanci kalubale daga abubuwan da bamu san dasu ba, har ma daga wadanda muke tare dasu. Sa’annan Idan kana da wani ilimi ko baiwa da Allah yayi maka, kar ka boye, kar kayi rowar sa, ka zama kamar su Dr. wajen taimakawa na kasa da kai masu tasowa, watarana bamu nan, abinda za’a iya tunawa damu shine abinda muka aikata, da mutanen da rayuwarsu tayi kyau sakamakon kalamanmu, ayyukanmu, ko dukiyar da muka bayar.
FAQs
Ta Yaya Aka Zabi Wadannan Influencer Din?
An zabe su ne ta hanyar kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar a dandalin Facebook, inda kowa ya zabi gwaninsa bangaren kawo cigaba ta bangaren Ilimi.
Zan Iya Following Dinsu A Wasu Platforms Din?
Eh Zaka Iya, yawancinsu suna amfani da different platforms kamar Instagram, YouTube, da TikTok, amma Facebook shine babban platform da muka tabbatar kowannensu yana yi. Ka kula wajen bibiyarsu a wani wajen, ka tabbar su dinne kuma.
Ta Yaya Zan Amfana Da Iliminsu?
Ka bibiyi shafukansu, ka ringa kallon videos dinsu da rubutun da suke yi (Contents), sa’annan ka ringa koya daga garesu ko shawarwarinsu don inganta rayuwarka.
Shin Akwai Wasu Influencers Da Ba’a Lissafa ba?
Sossai ma kuwa, sune suka fi yawa watakila. Domin ta iya yiwuwa akwai wanda duk yafi su amma bai shiga list din ba. Domin an fitar da wannan sakamakon ne ta hanyar amfani da wanda mutane sukafi zaba.