Get Our Free New Course >> Artificial Intelligence Program.
HomeNewsYadda Anthony Joshua Ya Yi Hatsarin Mota A Najeriya Da Mutuwar Abokansa

Yadda Anthony Joshua Ya Yi Hatsarin Mota A Najeriya Da Mutuwar Abokansa

  • December 30, 2025

Anthony Joshua, tsohon zakaran dambe na duniya wanda ya shahara a duk fadin duniya, ya shiga wani mummunan hatsarin mota a Najeriya a ranar 29 ga Disamba, 2025, yayin da yake mota a kan Lagos–Ibadan Expressway a Ogun State. Wannan lamari ya janyo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta da kafofin watsa labarai na duniya.

Me Ya Faru A Hatsarin?

A ranar Litinin da misalin karfe 11:00 na safe (agogon Najeriya), motar Lexus SUV da Anthony Joshua ke ciki ta yi hatsari yayin da ake zargin tana gudu fiye da kima (overspeeding). Inda direban ya kubuce masa sa’annan ya ci karo da wata babbar mota ta tayi parking kusa da hanya.

Hatsarin ya faru ne yayin da Joshua da tawagarsa suka shigo Najeriya domin ziyarar yan uwa da abokai (holiday) kan bukukuwan kirsimeti da kuma bikin new year,

Abin Da Ya Faru Da Joshua

Anthony Joshua, wanda aka fi sani da AJ, ya ji kananun rauni a lokacin da abin ya faru, kuma an kai shi asibiti nan take domin a duba lafiyarsa. Anyi nasara dan wasan yana cikin yanayi mai kyau, ba’a mummunan hali ba.

Mutuwar Mutane A Cikin Hatsarin

Abin takaici, mutane biyu, abokansa kuma membobin tawagarsa sun mutu nan take a wurin hadarin. Sun hada da:

  • Sina Ghami — Shine coach mai horarwa (Strength & Conditioning Coach)
  • Kevin Latif “Latz” Ayodele — Personal Trainer sa’annan kuma abokin aikin AJ.

Wadannan mutane biyu sun kasance suna da kusancu tare da Joshua, tun daga fagen career dinsa har izuwa bangaren rayuwarsa.

Abinda Hukumar Tsaro Ta Bayyana

Hukumar Federal Road Safety Corps (FRSC) ta bayyana cewa hatsarin ya biyo bayan gudu mai tsanani da motar takeyi a hanya, wanda na daga cikin manyan dalilan dake haidar da hatsuran mota a manyan hanyoyin Najeriya.

Martanin Jama’a Da Shugabanni

Bayan labarin ya bazu a kafafen duniya:

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mika gaisuwar sa ga dan wasan wato Joshua a asibiti tare da fatan waraka.
  • Masu fafutuka da masoya daga bangarorin daban-daban sun yi ta mika sakonnin ta’aziyya ga dan wasan.
  • Sa’annan Kuma an samu gaishe-gaishen ta’aziyya daga sauran ‘yan dambe da abokan aikinsa a duniya baki daya.

Me Wannan Lamari Ke Nuna Mana?

Wannan hatsari ya jawo tambayoyi masu zurfi game da:

  • Tsaron hanyoyi a Najeriya da Afrika baki ɗaya
  • Bukatar inganta dokokin zirga-zirga
  • Muhimmancin tuki a hankali da bin ka’idojin hanya
  • Kuma ya nuna cewa har da manyan shahararrun mutane ma ba su tsira daga hatsarorin mota ba.

Leave a Comment

Simas Academy Ta Kaddamar Da Sabon Course Na Video Content Creation A Hausa Domin Koyar Da Content Creation Da Dogaro...
Learn How To Check BVN Number Using A Code That Works Fast. A Complete Guide On Safe, Quick, And Reliable...
In a futuristic reflection on the rise of Artificial Super Intelligence (ASI), Nigerian tech thinker Aliyu Saidu Jauro has declared...
Who Are The Top Richest Crypto Traders In Africa? And The Richest Forex Traders In Africa? As We Dive In...