Curriculum
Course: WordPress Web Development [Hausa]
Login

Curriculum

WordPress Web Development [Hausa]

Video lesson

Introduction To The WordPress Web Development

Lesson video progress:
0%
of
100%

Maraba Da Zuwa Duniyar WordPress

Assalamu Alaikum, Barka Da Kasancewa Tare Da Ni! A Wannan Karatu Na WordPress Web Development.

Sunana Aliyu Saidu Jauro,
A Wannan Course Din, Za Mu Koyi Wasu Abubuwa Masu Muhimmanci Wadanda Zasu Bude Mana Ƙofar Shiga Duniyar Yanar Gizo.

Kana Yawan Jin Website, Website, Website, Ko Na Labarai, Ko Na Daukar Aiki, Ko Na Sada Zumunta. Amma Shin Ka Taɓa Tunani Ko Ka Taɓa Ganin Yadda Ake Gina Website? Ko Kuma Wannan Shine Karon Farko Da Ka Ji Labarinsa?

Ko Da Wannan Shine Karonka Farko, Ka Kwantar Da Hankalinka, Domin Za Mu Fara Daga Matakin Farko, Har Izuwa Matakin Da Kaima Zaka Iya Hada Taka Website Din.

Me Za Ka Iya Samu Daga Wannan Course?

  • Za Ka Fahimci Menene Website Da Yadda Yake Aiki

  • Zaka Koyi Amfani Da WordPress CMS Wajen Hada Duk Wata Website Da Kake Bukata

  • Za Ka Samu Kwarewa Akan Amfani Da Hosting Da Kuma CPanel

  • Za Ka Koyi Amfani Da Localhost A Computer Ka Idan Kana Da Ita

  • Kuma Zaka Koyi Amfani Da Themes, Plugins, Da Sauran Abubuwa Masu Muhimmanci Don Gina Website Mai Kyau

  • Zaka Samu Ilimi Kan Wasu Kalamai Da Ake Amfani Dasu A Duniyar Yanar Gizo

  • Bugu Da Kari, Zaka Hadu Da Mutanen Da Suke Da Kwarewa Da Ra’ayi A Wannan Bangaren Domin Inganta Tafiyarka

  • Daga Karshe Zaka Koyi Hanyoyin Da Zaka Bi Wajen Yin Amfani Da Wannan Ilimi Domin Samun Na Dogaro Da Kai A Internet

Wannan Course An Yi Shi Ne Musamman Don:

  • Sabbin Masu Sha’awar Gina Website, Watakila Saboda Kasuwancinsu, Kamfanin Da Sukeyiwa Aiki, Gwamnati, Ko Kuma Samun Monetization Ana Biyansu Daga Wasu Kamfanoni Irinsu AdSense, Monetag, Ezoic, HB Agency, AdsTerra, Tallads Da Sauransu.

  • Har Ila Yau An Yi Shi Ne Ga Matasa, Matan Gida, Ko Yan Makaranta, Da Duk Wanda Ke Sha’awar Samun Sabon Skill, Ko Hanya Ta Kasuwanci Ko Bayar Da Bayanai A Intanet.

  • Da Kuma Wadanda Ba Su Da Ilimin Coding Ko Fasaha Amma Suna Son Su Koya, Wannan Duka Naku Ne.

Shiyasa Abinda Nakeso Da Ku Shine, Mayar Da Hankali Wajen Bibiyar Da Fahimtar Komai. Munyi Shi A Saukake Ta Yadda Kowa Zai Iya Ganewa. Muje Zuwa…