Ko ka san ana samun kyautar data daga Simas Academy? Ba wai kawai koyar da ilimin fasaha da zamani ake yi ba Simas Academy, hatta regsiter idan kayi ko ka gayyato wasu sukayi rajista, ko kuma ka fara karatu ko ka kammala darasi a cikin course ko program, zaka rika samun kyautar data kai tsaye. Wannan tsarin an kirkiro shi ne domin karfafawa dalibai gwiwa, da kuma tabbatar da cewa makarantar ta bada abinda ake so wato sakamako.
Ga yadda tsarin yake idan kana bukata, ba wahala:
Ta Yaya Tsarin Kyautar Data Ke Aiki?
Tsarin kyautar data na Simas Academy yana aiki ne ta hanyar points (wato Point System). Kowane dalibi ko mai ziyartar website din idan ya yi wani abu mai kyau sai a ba shi points a matsayin lada. Wadannan points din su ne ake mayarwa kyautar data domin ka ci gaba da amfani da intanet kyauta.
Wannan yana nufin, ba lallai sai ka kashe kudi wajen sayan data ba, kawai ka kasance active da kuma ayyukan da suka dace a dandalin, ka rika tara points. Wannan tsarin ya kara bambanta Simas Academy da sauran makarantun zamani, domin ya hada ilimi, nishadi, gasa, da kuma lada a lokaci guda.
Abubuwan Da Ke Bada Points
Kafin ka shiga dandalin, yana da kyau ka fahimci abubuwan da suke bada points din, wanda idan kayi zaka ringa samu.
- Register (500MB): Na farko, da zarar ka bude account a Simas Academy wato register, kai tsaye za’a fara baka kyautar 500MB. Wannan yana nufin ma kafin ka fara karatun ka samu kyautar.
- Sayan Courses (500MB): Duk lokacin da ka sayi wani course ko ka shiga program shima zaka samu 500MB kyauta.
- Yin Assignment (150 Points): Bayan kayi wani karatu na darasi, idan aka baka assignment ka yi kuma ka haye to zaka samu 150 Points na data. Wannan yana karfafawa dalibai wajen mayar da assignments da matukar muhimmanci.
- Kammala Course (3GB): Wannan shi ne lada mafi tsoka da ake samu a Simas Academy. Da zarar ka kammala karatun wani course gabadaya, zaka samu 3,000 Points wanda yake daidai da 3GB. Wannan kyauta ce ta musamman ga dalibai masu dagewa, idan ka kammala courses goma kenan kana da 30GB kyauta, lallai Simas Academy makarantace ta musamman.
- Wuce Quiz (100MB): Idan ka yi quiz kuma ka wuce, zaka samu 100 points. Shi quiz ba dole sai kana karatu a Simas Academy ba, lokaci zuwa lokaci ana iya sake Quiz kowa yazo ya zuba iliminsa.
- Wuce Quiz Da 100% (200MB): Duk lokacin da ka wuce quiz da 100% ba tare da ka fadi ba, Whoa! zaka samu karin 200MB kyauta. Wannan shi ne tsantsar lada ga mutanen da suka fi dagewa koda ba daliban Simas Academy bane su.
- Kammala Darasi (10 Points): Duk lokacin da ka gama lesson, zaka samu Points 10. Duk darasi yana da lada, don haka koda kadan kake yin gaba, ka san kana tara lada.
- Samun Aboki (50 Points): Idan ka kulla abota da mutum wato katura friend request ya karba, zaka sami 50 points shima zai samu. Wannan tsarin yana karfafa hadin kai da zumunci masoya Simas Academy.
- Shiga Group (10 Points): Duk lokacin da ka shiga wani group, zaka samu Points 10.
- Affiliate Registration (200MB): Idan ka gayyato wani ya yi rajista da link dinka, zaka samu 200MB. Wannan na nufin duk wanda ka turawa kuma ya shigo ta hanyar yayi register zaka samu 200MB kyauta. Koda mutane 20 ne daga cikin abokanka ka gayyato kowanne zaka samu 200MB.
- Affiliate: Sayan Course (500MB): Idan wanda ka gayyato ya , kai ma zaka samu karin maki 500. Wannan yana nuna cewa Simas Academy na daraja waɗanda suka taimaka wajen yada ilimi.
- Affiliate: Unlimited Data (100% Free): A Wannan tsari zaka ringa tara points ne ta hanyar samun wani kaso daga cikin abinda wadanda ka gayyato suke samu. Misali, idan ka gayyato abokinka, sai ya samu 1GB, to kaikuma zai kasance kana da 300MB. Duk lokacin da ya samu ya kai 10GB kaima kana da 3GB naka daban. Haka idan mutane da yawa ka gayyato.
Me Yasa Simas Academy Ta Kirkiro Da Wannan Tsarin?
Simas Academy tazo ne da manufofi na zahiri, wadanda babban burinmu shine mu tabbatar da cewa duk wani wanda ya koyi abu a makarantar ya karu. Sa’annan ba wannan bane kadai, muna so a koda yaushe mu kasance muna karawa dalibanmu kwarin gwiwa ta kowace hanya. Wannan tsarin kyautar data yana tabbatar mana da cewa karatu a Simas Academy bai tsaya iya kan abu daya ba.
- karfafa Kwarin Gwiwa: Dalibi baya jin karatu yana da wahala idan yana ganin points na taruwa.
- Inganta Abota Da Zumunta: Ana samun points ta hanyar yin abokai da shiga groups.
- Himma Wajen Fahimta: Wannan yana sa masu yin assignments da quizzes su sanya himma sossai wajen ganin su samu sakamako.
- Taimakon Juna: Affiliate system yana bada damar gayyato wasu, wanda kowa zai mori wannan tsarin.
Ta Yaya Za Ka Fara?
- Ka shiga shafin Simas Academy ka yi regsiter, mafi sauki da Google account dinka.
- Ka nemi course da kake da ra’ayi sa’annan ka fara karanta shi.
- Ka shiga forum, sa’annan ka ringa interacting da mutane.
- Ka gayyato abokai, yan uwa da danginka ta hanyar affiliate link dinka.
- Ka cigaba da karatu har ka kammala course domin samun cikakken points dinka.
Daga Karshe
A Simas Academy, ba kama hannun yaro wajen karatu da samar da garabasa ga dalibai dama wadanda basu shigo ba. Kowa yana da damar da zai iya zuwa Simas Academy sa’annan yaci moriyarsa. Wannan tsari na kyautar data yana da saukin fahimta, da saukin samu, kuma yana tabbatar da cewa duk dalibi zai ji cewa yana da muhimmanci a kowanne mataki na tafiyarsa.
Babban abinda bamu so a nan shine Yaudara! Duk wanda aka kamashi da laifin zamba ta kowacce hanya zai rasa account dinsa gabadaya.
FAQs: Tambayoyi Da Ake Yi Game Kyautar Data
Shin Duk Wanda Ya Yi Rajista A Simas Academy Zai Samu Data?
Eh, duk wanda ya bude account zai sami kyautar 500MB kai tsaye a matsayin maraba da zuwa makarantar Digital school na Simas Academy.
Ta Yaya Ake Lissafa Data Na Points Da Nake Tarawa?
Ana lissafa shi ta hanyar points system. Points din da kake tarawa suna juyawa zuwa data. Misali, 100 points = 100MB.
Shin Zan Iya Tara Data Da Yawa?
Kawarai kuwa, zaka iya tawarawa babu iyaka. Yawan datan da zaka samu ya danganta da yawan ayyukan da kake yi a shafin.
Idan Na Kammala Course Daya, Zan Samu Data Nawa?
Kai tsaye zaka samu 3000MB (3GB) a matsayin babbar kyauta daga Simas Academy.
Shin Affiliate Yana Aiki Yadda Ake Samun Data?
Tabbas, idan ka gayyato wani ya yi register da link dinka zaka samu kyautar 200MB, duk lokacin da ya sayi course kuma zaka samu 500MB. Haka zalika duk wani abinda ya samu zaka ringa samun 20% daga ciki.
Idan Na Ci Quiz 100% Zan Samu Karin Points Ne Na Daban?
Idan kaci Quiz gabadaya 100% zaka samu 200MB madadin 100MB. Karin 100MB Za’ayi maka.
Shin Kyautar Data Ana Bada Ta Kai Tsaye Ne Ko Ana Jira?
Babu wani jiran da zakayi matukar kana da Data points kuma ka nemi Withraw. Nan take za’a tura maka ta layin da kake bukata, shikenan!
Koda Ni Ba Dalibi Bane (Ban Sayi Course Ba) Zan Iya Samu?
Eh, duk wanda ya shigo Simas Academy zai iya samu. Saboda haka koda kai ba dalibi bane idan kaci gaba da shiga Quiz, ko kuma kana gayyato mutane zaka samu Alherin Simas Academy.
Shin Wannan Tsarin Na Dindindin Ne Ko Na Lokaci Kaɗan?
Tsarin kyautar data yana nan daram, saboda yana daya daga cikin tsarin mu na gina dalibai a na makarantar zamani Simas Academy.