Email Marketing wata hanya ce ta kasuwancin zamani wato Digital Marketing wacce ake amfani da ita wajen aika sakonnin email ga customers da masu sauraro. Wannan dabarar ta kasance daya daga cikin tsofaffin hanyoyin Digital Marketing, amma har yanzu tana da karfi da kuma tasiri sosai saboda tana ba da damar sadarwa kai tsaye tsakanin dan kasuwa da abokan cinikinsa wato customers.
Menene Email Marketing?
Email Marketing hanya ce ta amfani da email na mutane wajen tura sakwanni, talla, ko bayanai ga customers cikin sauki. Email Marketing na nufin tara jerin email na mutane (wanda ake kira da subscribers), sannan ka ci gaba da sanar da su sabbin kayayyakinka, ayyukanka, saukin farashi, ko ilimantar dasu.
Misali, Idan ka sayi kaya daga Temu ko ka bude account dasu, za ka ga suna turo maka email suna cewa ga kayayyaki masu sauki, ga sabbin abubuwan da suka kawo da sauransu. Wannan shi ne yadda email marketing ke a aiki.
Me Ya Sa Email Marketing Yafi Da Tasiri?
Email marketing yana da tasiri ne saboda kai tsaye kake magana da mutum. Ba kamar social media ba inda mutum zai iya rasa tallanka ya tsallake a cikin posts. Email kuwa yana shiga wayar mutum ne kai tsaye, kuma ana daukar sakwannin Emails da muhimmanci fiye da social media notifications.
- Ana iya amfani da wannan ilimi wajen gina dangantaka da customers (wato relationship).
- Yana ba da damar tura da tallace-tallace kai tsaye ba tare da ka biya kudi ba.
- Yana da arha idan aka kwatanta da talla a social media marketing ko talla (wato social paid ads).
Misali: Wani dan kasuwa mai sayar da kayan kwalliya na mata zai iya tara imel din customers dinsa. Duk lokacin da ya kawo sabbin lipsticks, sai ya turo sako ta email da hotuna da farashinsu. Wannan zai sa su dawo su saya saboda sun amince da shi.
Haka zalika da akwai email marketing tactics da ake amfani dasu, zai iya cewa, saura Lipsticks guda 100 suka rage a stocks, ayi sauri a saya kafin su kare. Ko kuma wani tactics din mai kama da wannan.
Ire-Iren Email Marketing
Wadannan sune ire-iren email marketing, wato types:
- Welcome Emails: Irin wannan Emails din na zuwa ne ga duk wanda ya shiga list dinka akaro na farko.
Misali: “Barka Da Regsiter A Simas Academy. Ga kyautarka matsayin sabon dalibi.” Anaso welcome email ya kasance bashida yawa, kuma ka tabbatar da cewa ka tarbe shi da sako mai kyau. - Newsletter: Wannan shikuma shine sanarwa ko labarai na kai tsaye da dan kasuwa yake yawan turawa. Ta iya yiwuwa kaima kana karban irinsu daga TikTok, Temu, Kuda, Selidia da sauransu.
- Promotional Emails: wadannan emails din Ana tura su ne lokacin da ake da discount wato rangwame ko kayayyaki na musamman da mutane suke nema. Temu suna yawan tura wannan da sauran ecommerce platforms, wato masu sayar da kayayyaki.
- Follow-up Emails: shikuma Idan mutum bai kammala wani abu ba, kamar sayan kaya, ko kammala payment, sai ka tunatar da shi. Ganin wannan Email din ka iya sanyawa ya dawo ya kammala, domin kuwa yana da tasiri.
Mutanenmu basu dauki Email marketing da muhimmanci ba. Abu ne mai sauki da yake da tasiri, domin duk kankantar business dinka, idan kana da email list ka gama komai. Influencers dinmu, yan kasuwanmu na gargajiya da zamani, malaman da suke koyar da courses, masu talla, makarantun mu, duk bamu mayar da hankali a kai ba. Amma shine the most profitable and effective digital marketing. Strategies din wanda duk ba wahala suke dashi ba wajen koyo, cikin wata daya zaka koyi skill din ka fara applying a cikin harkarka ka kalli sauyi.
Matakan Da Ake Bi Domin Nasara
- Gina Emails (Subscribers): Kada ka saka mutanen da baka sansu ba a list dinka (wato karka zama mai kwashe-kwashe, duk wanda email dinsa ya shiga to ya kasance yana da ra’ayin abinda kake sayarwa ko yi).
- Tsara Lists (Wato Segmentation): wannan wani tsari ne da ake bi wajen tsara list daki-daki bisa ga ra’ayinsu. Misali idan kana sayar da kayan maza da mata, to ya kasance mata list dinsu daban, maza list dinsu daban. Duk lokacin da ka tashi idan kayan mata ne zallah, sai ka tura musu, idan kuma general ne saika hadasu gabadaya.
- Ka Ringa Tura Sako Masu Jan Hankali: Kada ka tsawaita rubutunka sosai, kayi shi gajere, straight to the point, mai ma’ana, kuma ya kasance yana da CTA.
- Ka Ringa Duba Analysis: Ta nan zaka gano wane email ne aka fi buɗdewa, wannene akafi shiga har ayi sayayya, sannan ka inganta kalarsa. Wanda baya daukar hankali sai daina amfani dashi. Shiyasa a kullum, a kowane field na digital marketing, A/B test yana da matukar muhimmanci.
Fa’idodin Email Marketing Ga ‘Yan Kasuwa
- Ba’a Kashe Kudi: Ba sai ka kashe kudade masu yawa ba zaka iya gina email list dinka cikin sauki, musamman ma a nan Nigeria.
- Aiki Da Cikawa: Idan kana neman aiki da cikawa ka nemi Email marketing, domin yana zuwa ne kai tsaye ga target dinka ba tare da hayaniyar tallace-tallace ba wato ads.
- Duba Sakamako: Ta wannan hanyar za ka iya sanin adadin mutanen da suka bude sakonka, suka danna link, ko suka yi sayayya.
- Yana Kara Amana: Idan kana tura email masu amfani, customers dinka ko clients dinka ko students dinka zasu kara daukarka da muhimmanci.
Kalubalen Da Ake Fuskanta Da Email Marketing
- Emai Yana Shiga Spam: Sakon ka iya shiga spam idan baka rubuta shi da kyau ba, zai shiga spam. Amma idan ka tsara shi da kyau babu abinda zai same shi.
- Rashin Bukatar Emails: Ta iya yiuwa ka ringa tura emails a tunaninka mutanen suna so, alhali kuma basu so domin baya musu amfani, daga nan zasu daina budewa. Shiyasa dole farko akwai bukatar ka karance su. Kuma duk mun bayyana wadannan abubuwa dalla-dalla a program dinmu na Email Marketing dake Simas Academy, inda muka dauko ilimi daga kanta Google masu Gmail muka bayyanata ga dalibanmu. Kaima kana iya zuwa kayi register yanzu ka samu ilimin Email marketing.
- Ba Kowa Ke Son Bude Email Ba: Tabbas Ba kowa ke son bude imel ba. Amma da akwai emails da suka kasance ba’a guje musu, ka tabbatar naka na daga ciki.
Zaka Iya Register Da >>> Email marketing Course saboda ka koyi ilimin cikin sauki.
Takaitaccen Shawara Daga Aliyu Saidu Jauro
Idan kana gudanar da kasuwancinka a wannan zamani, to karkayi wasa da Email Marketing. Zan iya cewa, email marketing ya zama dole a gareka, koda wane irin sana’a kake matukar ta shafi zamani. Koda karamar sana’a ce kake yi, tara email list na customers dinka da masu ra’ayin kayanka zai iya haifar maka da ribar da baka taba zato ba. Abin da ake bukata shi ne ka koyi strategies na tsara emails din, da tura emails masu amfani, jan hankali, da kuma yin hakan akai-akai.