Get Our Free New Course >> Artificial Intelligence Program.
HomeHausaMenene Ma’anar SEO Da Yadda Take Aiki [You Need To Know]

Menene Ma’anar SEO Da Yadda Take Aiki [You Need To Know]

Ma’anar SEO itace hanyar da search engines irinsu Google suke bi su gano website da abinda ake wallafawa a cikin website din. SEO abu ne da mutane da yawa suna ji ana ambatawa, amma ba kowa bane ya san ma’anarta da yadda take aiki ba. Wasu suna daukar SEO kamar wani sirri ne na yanar gizo, wasu kuma suna daukarsa kamar wani abu ne mai wahala da sai manyan kwararru ne kawai za su iya gudanar dashi.

Amma gaskiyar magana ita ce, SEO abu ne mai sauki idan aka bayyana shi ta hanyar da kowa zai gane, musamman idan kai sabo ne ko kuma ba ka da wata kwarewa a harkar website, blogging, ko internet gabadaya.

A yau, za mu yi bayani dalla-dalla a kan Ma’anar SEO da yadda yake aiki. Idan ka tsaya har karshe zaka fahimci menene SEO, dalilin da yasa take da muhimmanci, da kuma yadda take aiki a zahiri.

Ma’anar SEO Da Hausa

Ma’anar SEO (Search Engine Optimization) na nufin hanyoyin da ake bi domin sanya website, blog, ko wani rubutu ya bayyana a Google ta yadda zai bayyana ga mutane a duk lokacin da sukayi searching.

A takaice, SEO ita ce hanyar da ke sa Search engines (Irinsu Google) ya gano ka, ya fahimce ka, sannan ya nuna ka ga mutane masu bukatarka.

Misali, idan wani yayi searching a Google:
Yadda ake samun kudi a internet

Google Search Simas Academy

Idan rubutunka da kayi a website dinka ya bayyana a shafi na farko, wannan ba sa’a ba ce. SEO ce ta aiki. Rubutu ne da aka tsara yadda Google zai fahimta kuma mutane za su amfana da shi. Shiyasa Google ta bayyana shi a sama.

Me Yasa SEO Take Da Muhimmanci A Wannan Zamani?

A yau, kusan duk abinda mutum yake nema yana farawa ne daga Google. Ilimi, aiki, kasuwanci, mafita, ko shawara, abu na farko da ake yi shi ne bincike.

Idan kana da ilimi, sana’a, ko kana kasuwanci amma babu bayananka a Google, ko kuma idan aka nemo ka a Google babu kai, to kamar kana magana ne a daki mai duhu babu kowa.

Ma’anar SEO A Gurguje:

  • Baiwa mutane damar ganinka
  • Samun traffic (Mutane) kyauta zuwa website dinka
  • Inganta amana a idon mutane da duniya baki daya
  • Taimakawa wajen samun kudi a online ta hanyar website

Wannan dalilin ne yasa Simas Academy ke jaddada SEO a matsayin digital marketing skills da yakamata ka koya.

Yadda SEO Take Aiki

Kafin mu gama fahimtar Ma’anar SEO, dole ne mu kara fahimtar yadda Google ke aiki.

Google ba ya tunani kamar mutum. Abinda yake yi shi ne:

  • Yana Iya karanta rubutu
  • Yana kokarin fahimtar me rubutun yake nufi
  • Sa’annan ya gwada shi da abin da mutane suke nema
  • Daga karshe ya bayyanawa wadanda suke searching dinsa

Idan rubutunka ya amsa tambayar mutum sosai, kuma an tsara shi da kyau, Google zai fara nuna shi.

SEO ba yaudarar Google ba ce, a’a. Taimaka wa Google ne ya fahimci rubutunka. Idan kayi kokarin yaudarar Google to gabadaya zasu dakatar da website dinka daga bayana a Search result.

Yadda SEO Ke Aiki A Zahiri

Da zarar ka wallafa rubutu ko post a website dinka, abu na farko da yake faruwa shi ne posting. Wannan yana nufin ka saka sabon content a internet, kamar labari, bayani, ko koyarwa.

Bayan haka, Google bots zasu fara crawling, wato suna zagayawa a intanet suna neman sabbin rubuce-rubuce. Idan suka gano shafinka, za su karanta abin da ka rubuta domin su fahimci me yake magana a kai.

Idan Google ya fahimci rubutunka, mataki na gaba shi ne indexing. A nan ne Google ke ajiye shafinka a cikin database dinsa, kamar yadda ake adana littafi a cikin library. Idan ba a yi indexing ba, rubutunka ba zai bayyana a search ba, watakila wajen crawling an kalli rubutun yana da matsala, kamar Copyright, low value content, da sauransu.

Daga nan sai ranking. Lokacin da wani ya nemi abu a Google, sai Google ya bayyana rubutunka da na wasu. Idan naka ya fi dacewa, ya fi amfani, kuma an tsara shi da kyau, zai iya bayyana a shafi na farko, wato a saman na sauran mutane

Google Search Yadda Seo Yake Aiki

A takaice, SEO tana tafiya ne a tsarin:
Posting → Crawling → Indexing → Ranking

Duk abin da SEO ke yi, manufarta ita ce a tabbatar Google ya fahimci rubutunka kuma ya nuna shi ga wanda yake nema. Muna koyar da ilimin SEO a Simas Academy ga duk dan kasuwa ko wanda yake neman skills na digital marketing.

Leave a Comment

Wadannan Sune Sana'o'in Mata Da Mace Zata Iya Yi Domin Ta Dogara Da Kanta A Wannan Zamani, Koda Budurwa Ko...
Mun Kammala Jerin Hausa Influencers 15 Da Suke Taimakawa Wajen Yada Ilimi A Nigeria A Facebook. Bangaren Fasaha, Rayuwa, Shawari...
Tarihin Sanusi Danjuma Ali, Tare Da Karatunsa, Iliminsa, Kalubale Da Kuma Ayyukan Da Yayi Bangaren Cryptocurrency, Trading.
Ko Ka San Ana Samun Kyautar Data Daga Simas Academy? Karanta Yadda Zaka Bi Wajen Samun Naka Unlimited Data GB...