A wannan zamani na ci gaban fasaha da yanar gizo, akwai dama mai yawa ga mata da zasu dogara da kansu ta hanyar sana’o’in zamani. Sana’o’in Mata Na Zamani sun hada da abubuwa da dama da mace zata iya yi a gida, ba tare da ta shiga wata hanya mummuna ko aikata wani abu da ya sabawa addini ko al’adu irin namu ba. A Yau zamu bayyanawa sana’o’i guda 15 da suka kasance sirri da na zamani da mata zasu iya yi domin su ringa samun na biyan bukata daidai gwargwadon kokarinsu.
Me Ya Sa Sana’o’in Zamani Suka Kasance Mafita Ga Mata?
A wannan zamani, rayuwarmu ta kara tsada, a dai-dai lokacin da karnin mu ke tsaka da juyawa kuma muke fuskantar sabuwar duniya. Farashin abinci, tufafi, kayan more rayuwa duk suna bamu wuya. Sai dai inda muke samun sauki shine sana’o’in zamani suna bamu dama, musamman matasa wanda idan ka duba zaka ga rayuwar da yawa sun samu kyakkyawar sauyi ba tare da dogaro da iya gwamnati ba.
Idan muka kai duba ga rayuwar mata a wannan zamanin zamu ga cewa lallai suna bukatar samun wadannan ilimin zamanin. Duba da yadda suke rayuwa a gidajen iyayensu ko mazajensu, Infact, ni a ganina mata sunfi bukatar ace sunfi maza rungumar ilimin Fasahar Zamani. Yanzu mun shiga wata revolution ne da ake ce mata 4IR, wato The Fourth Industrial Revolution, inda ilimi musamman na fasaha shine arzikin mutum, ba kamar baya ba. Sarki Goma Zamani Goma.
Dukda cewa da akwai mata musamman matasa da tuntuni sunyi nisa a cikinta irinsu Zainab Saidu Idris, Hajaru Muhammad, Amina Ibrahim Idris, Da sauran da yawa, zamu ga sun samu kyakkyawar sauyi kuma suna taimakawa yan uwansu mata da yawa.
Da shike sabbin abubuwa ne na zamani, da fasaha suka kawo mana yasa mutanen mu basu dauki abun da muhimmanci ba. Sa’annan kuma mu abinda suke zuwa mana yawanci harkokine na damfara, inda za’azo a ja mutane amma a yaudaresu. A bisa haka yasa ba kowa bane yake yarda ko yake iya bayyana su, ko kuma yayi bincike a kansu har yayi tunanin cewa yakamata ace mata suna wadannan harkokin. Bari mu lissafo sana’o’i guda 15 da mace zata iya zaba daga ciki ba tare da bata lokaci ba:
Kasuwancin Online (Online Business)
Na faro, Kasuwancin Online na nufin mace ta samu wani products wato kaya ko service wato aiki, da zata ringa tallata shi a online kuma ana saya tana turawa. A yanzu, mace na iya bude shagonta a yanar gizo ta hanyar amfani da social media platforms kamar Facebook, Instagram, WhatsApp ko Tiktok, na tabbata zuwa yanzu da akwai matan da suke samun miliyoyi kowacce shekara daga online (Ya danganta da harkarsu).
Ana iya sayar da kaya kamar kayan kwalliya, kayan sakawa, ko kayan gida, wasu matan har abinci suke sayarwa irinsu awara, kaza, da sauran kayan makulashe. Wannan hanya ce mai sauki da ba sai kana da jari mai yawa ba zakayi. Baka bukatar physical location, ko kudin talla, ko mai’akata a tashin farko.
Blogging Ko Content Creation
Idan kina iya rubutu ko hada video mai jan hankali, blogging ko content creation na iya zama sana’ar da zai samar miki da kudin shiga musamman idan kika iya shi. Blogging ta kasance sana’ata, bata da matsalar fahimta kuma idan aka jure aka koye ta tana samar da yanci.
Ba kowane ya san da harkar blogging ba a mutanen mu, hakan ne yasa personally nake bada mentorship (Training) kyauta kowacce shekara > zaku iya min magana a shafina na Facebook ko Instagram idan kuna ra’ayi kuma da akwai fili, Aliyu Saidu Jauro.
Freelancing
Na uku shine Freelancing kamar yiwa mutane aiki suna biyanki, kamar rubutu, editing, graphic design, ko data entry, SEO service, Web Design ko Development, duk wadannan na daga cikin sana’o’in zamani da mace zata iya yi.
Shekaru ina aikin SEO Service inda nake yiwa masu business website optimazation suna biya na. Sai dai kuma zuwan AI a yanzu ya ragewa aikin freelancing karfi, wanda yanzu kusan kowa yana amfani da AI wajen kammala aikinsa da kansa, amma duk da haka mutum yana iya zakulu abinda yake da daraja ya zuba lokacinsa, kudinsa da karfinsa ya koya.
Social Media Management
Social Media, wannan babbban harkace, kuma zan iya cewa sirri ne da ba kowa ya san ta ba. Amma ina mai tabbatar muku da cewa Social Media Management zaizo ya zama daya daga cikin manyan harkokin internet nan gaba. Kun san meyasa? Saboda yanzu mutanenmu da yawa sun fara wayewa da bude kasuwancinsu a online, haka zalika yan siyasa, manyan kamfanoni, da sauransu.
Social Media Management shine kula da shafukan yanar gizo na wani kamfani ko wani mutum, ta iya yiwuwa dan siyasa, dan kasuwa, dan kwallon kafa, shugaba ko Mallami. Social Media Managers ake kiransu kuma ana amfani ne da ilimin Social Media Marketing wajen gudanarwa da kuma ilimi a kan abinda za’a ringa wallafawa, Za’a iya samun cikakken wannan ilimi na Social Media Marketing wato SMM a makarantar Simas Academy ta hanyar zuwa kayi register da program din. Ko kai tsaye ka shiga ta nan >> Social Media Marketing Course.
Graphic Design
Na biyar, Graphic Design, wanda zan iya cewa kusan kowa ya sanshi saboda matasanmu da yawa suna harkar maza da mata. Duk da cewa harkace da tayi suna kuma ana samun na biyan bukata, amma tana da competition sossai wato kasuwace da akayi yawa.
Graphic Design aikine da wani ko kamfani zasu baka aikin hada musu hoton kayansu, watakila poster, flyer, banner din talla ko kuma logo, da sauransu. Muna iya ganin ire-iren wadanndan a social media kullum ana talla da poster, ko na dan siyasa, ko graduation, ko invitation card da sauransu.
Affiliate Marketing
Affiliate Marketing, amma ba affiliate marketing na yan 419 da ake yiwa mutanenmu ba da sunan Affiliate Marketing. Asalin Affiliate Marketing harka ce da kai tsaye zaka ringa zuwa Online Stores irinsu Seledia, Amazon, Ebay, Jumia, ClickBank, da sauransu kana dauko kaya kana tayasu talla su kuma suna samun customers suna biyanka.
Ba lallai sai manyan kamfanoni ba, kina iya zuwa kananan kamfanonin sayarda kaya ko waya da sauransu ki tambayesu ko suna da affiliate program. Idan akwai sai su baki dama, inda zaki zo ki ringa tallatawa ba tare da kin mallaki kayan ba, kuma duk wanda ya saya ta sanadinki kina da commission. Amma yin hakan dole ya kasance kina da mutane.
Local Production
Muna da mata masu basirar yin abubuwa da yawa, wasu suna iya hada yan kunne, sarka, warwaro, kayan turare, huluna da sauransu. Amma ba kowa bace take iya zuwa online ta inganta ba. Inda zata iya haduwa da wasu business owners din tana sarar musu. Koda baki iya ba idan kina da ra’ayi kuma kina da wajen da zaki koya ko wacce zata koya miki kina iya koyo kiyi amfani da kasuwancin zamani wajen tallafawa kanki.
Tailoring
Kasuwancin Tailoring wato dinki ya samo asali tun daga zamannin kakannin kakanni. Kuma har yanzu yana nan, sa’annan har izuwa gobe zai cigaba da kasancewa. Sai dai a kowane lokaci zai ringa tafiya ne da zamaninsa. Saboda haka ne yasa Tailoring ya zama daya daga cikin sana’o’in da mace zata iya koyo kuma ta dogara da kanta a wannan zamani.
Bugu da kari, teloli suna iya amfani da ilimin kasuwanci da fashar zamani wajen bunkasa kansu. Musamman ma idan kin iya dinki mai kyau, kina iya collaboration da wani fashion company ko ko incluencer kina sayar da kayanki da daraja. Ga wadanda suke da ra’ayin bunkasa kansu, suna iya koyawa na kasa dasu ko su dauki wasu aiki suna dinka kayayyakin suna sayarwa da yawa lokaci guda a kyakkyawar farashi. Hakan zaki zama kamar kamfanine da kanki. Akwai bukatar ki bude tunaninki da lissafinki domin zuwa waccan matakin.
YouTube Channel
YouTube daya ne daga cikin kasuwancin zamani da mace zata iya yi a cikin gida ba tare da wani takura ba. YouTube na daya daga cikin manyan manyan hayoyin da suke samarwa al’umma kudaden shiga, inda idan mutum yana sanya bidiyo masu daukar hankali zai ringa samun revenue kowane wata ana biyansa daga Google Adsense, ko makamancin wannan.
Duba misali da yadda harkar Kannywood da Nollywood suka koma YouTube, kun san me yasa? Ba komai ba saboda irin kudaden da suke samu kowane rana, musamman manya-manyan fina-finai irinsu Labarina Series, Izzar So, da sauransu. Shiyasa suma kansu ba zasu so fim din ya kare ba saboda makudan miliyoyin da suke samu kowane wata. Da akwai mata da yawa da suke harkar YouTube, wasu novels suke karantawa, wasu labarai suke sakawa, misali Voice of Anani da sauransu.
Digital Marketing
Na goma shine shi kansa Digitall Marketing din, wato kasuwancin zamani. Wannan ilimi ne da mutum zai koya game da kasuwancin zamani saboda ya koyar, ko yayiwa mutane aiki dashi ko kuma yayiwa kansa aiki dashi. Digital Marketing ya tara ilimi da yawa wanda kamfani ko wata organization tana iya daukar mutum aiki.
Virtual Assistant
Masu kasuwanci ko mutane da yawa suna neman wadanda zasu ringa taimaka musu da ayyuka irinsu email marketing, tsara jadawalin aiki, ko customer support da sauransu. Wannan aiki ne da Company zasu baka role kaikuma ka ringa kula dashi. Misali, just recent Simas Academy ta dauki virtual assistant mata guda 2 wadanda zasu ringa kula da matsalolin dalibai, duk wanda yake da matsala kai tsaye idan yayi magana sune zasu magance matsalar.
WhatsApp Business
WhatsApp Business ba ina nufin WhatsApp business na app ba, a’a, wannan wani Business Model ne na musamman da mutane suka kirkirota. Yadda kasuwancin yake shine, mutum zai bude WhatsApp account, ya bude groups da channels yana dora abubuwa na daukar hankali, sa’annan ya ringa tara lambobin mutane (organic and active) yana saving sa’annan yana sanyasu suna saving. A haka zai tara mutane dubbai, saboda da akwai abubuwan da ake yi na jan mutane.
A haka duk lokacin da ya dora wani abu ko talla, ko affiliate link zai ringa samun commission. Irinsu ne ake basu talla a WhasApp sai su dora, domin ana samun dubunnan mutane masu kallo.
Cryptocurrency
Crypto na daya cikin kasuwancin da suka shahara a yan shekarun nan musamman a Nigeria sakamakon zuwan Airdrops ko Mining. Sai dai kuma harkar Cryptocurrency da mining akwai banbanci, duk da cewa mining din yana karkashin Crypto ne gabadaya.
Ita Cryptocurrency harkace da zakiyi amfani da kudinki ki shiga kasuwa (ana kiranta da exchange) inda zakiyi amfani da ilimi wajen nemo tokens ko coins da darajarsu zasu iya tashi sa’annan ki saya ki ajiye zuwa lokacin da kike tunanin tashin nasu zai zo ki sayar. Wasu currencies din suna iya tashi a cikin awanni, wasu kwanaki, wasu na kai sati wasu watanni, wasu har shekaru suna iya rikewa su jira tashiwarta (amma yawanci irin wadancan suna iya canjawa mutum rayuwa misali Solana, lshekaru kadan baya kwata-kwata bata wuce Naira dubu daya ba, amma yanzu kowacce guda farashinta yana buga sama da 300,000 a lalace, yi lissafi idan a wancan lokacin kin sayi guda hamsin ko ashirin, hakama Bitcoin wanda yau darajarsa ta haura naira miliyan 180, haka Etherium da sauransu).
Wannan crypto kenan, sai dai harkace da take da hatsari sossai shiyasa kake bukatar ilimi da malami kafin ka fara sanya kudinka ka sayi wani abu, kamar sayan Gold ne. Idan kaje makaranta irinsu Bitkova zasu baka cikakken ilimi game da Crypto.
Kiwo
Kwarai ma kuwa kiwo, kiwo na daga cikin kasuwancin da ake yinsu tun zamanin kakannin-kakanni, amma muddin kina da ra’ayin kiwo kuma kina da ilimi a kai to tabbas zaki iya bunkasa shi ki zamanantar dashi sa’annan ki ringa taimakawa kanki dashi. Da akwai wadanda suke amfani da fasahar zamani da yawa wajen inganta kasuwancinsu na kiwo, watakila kifi, nau’ukan kaji, tumaki, da sauransu.
Koyarwa (Coaching)
Ba iya a zahiri ake koyarwa ba, yanzu koyarwa ta koma internet wato digital. Shiyasa muke samun karbuwan makarantun zamani irinsu Malamiromba, Simas Academy, Bitkova, Flowdiary, da sauransu. Muddin kina da wata ilimi kina iya bude ajin da zaki koyar, ko kuma mafi sauki ki duba makarantar da take koyar da abubuwan da kike da kwarewa a kai sa’annan ki nemi kasancewa Tutor, misali mu nan Simas Academy a koda yaushe kofa a bude take.
Daga Karshe, Wadannan sune sana’oin mata na zamani da muka kawo da mata zasu iya yi daga cikin gidanjensu ba tare da dogaro da wasu ba hattan mazan ma. Muddin aka sanya niyya kuma aka dage In Sha Allahu labarin zai sauya. Da akwai wasu kalubule a tashin farko, wannan kuma dole ne a kowacce harka ko rayuwa . Amma muddin aka jure akayi tsaka tsan-tsan za’a samu abinda ake so.
Zamani idan tazo dole a bita, duk wanda yayi gardama kuwa za’a barshi a baya. Shiyasa aka samar da makarantar Simas Academy ta zamani inda zakayi amfani da wayarka ka koyi ilimiin digital skills daga wayarka cikin sauki.