Have a question?
Message sent Close

Tarihin Sunusi Danjuma Ali, Karatu, SCTV, & Net Worth

Tarihin Sunusi Danjuma Ali Crypto

Table Of Contents

Tarihin Sanusi Danjuma Ali, Tare Da Karatunsa, Iliminsa, Kalubale Da Kuma Ayyukan Da Yayi Bangaren Cryptocurrency, Trading.

A Nageria, musamman arewacin kasar, akwai sababbin fitattun matasa da suka rungumi fasahar zamani a matsayin hanya ta nasara. Daga cikinsu akwai Sunusi Danjuma Ali, hazikin matashi wanda ya tabbatar da cewa ilimin zamani na iya zama makamin da zai canja rayuwar mutum gaba daya. Labarinsa abin koyi ne ga duk wanda ke mafarkin shiga harkar internet da fasahar zamani domin neman rufin asiri da kuma tasiri ga al’umma gabadaya. Bari kuji labarinsa da na hada:

Wanene Sunusi Danjuma Ali?

Sunusi Danjuma Ali haifaffen garin Minjibir, Kano, Nigeria ne, wanda aka haife shi a ranar Talata, 3 May, 1988. Matashi ne mai hangen nesa wanda yana daga cikin wadanda suka kawo sauyi mai kyau a duniyar Internet a Nigeria, dama Africa baki daya. Yayi suna a bangaren kasuwanci na zamani, musamman a harkar cryptocurrency, blockchain, da digital marketing. Rayuwarsa ta sha banban da yawancin matasa, domin ya tashi da kyakkyawar tsari, ya kuma tsallaka matakai daban-daban kafin ya kai matsayin da yake a yanzu.

BayaniCikakken Bayani
Asalin SunaSunusi Danjuma Ali
Shekarun Haihuwa3rd May, 1988
Wurin HaihuwaMinjibir, Kano, Nigeria
Sana’aCryptocurrency, Kasuwancin Zamani (DM), Da Noma
NationalityNigeria
IlimiMsc, Degree A Fannin Kasuwanci
Shaida (Title)Msc, Jagoran Crypto, Bitget Global Ambassador
Mu’amalaYana Da Aure
Notable ProjectScTV (Sunusi Crypto Television) Africa

Educational Career

Sunusi ya yi karatun Primary da Secondary a Kano. Bayan wannan ya wuce zuwa jami’a, inda ya yi Degree a fannin kasuwanci (Business) da kuma zurfafa binciki da neman ilimi a fannin fasahar zamani wato Internet & Digital Knowledge. Wannan ya bashi damar hada karatun zamani da fasahar zamani wanda hakan yasa ya samu kyakkyawar ilimi mai inganci.

Nysc With Sanusi Danjuma Ali
Manomi mai Bautar Kasa

Haka zalika, ya halarci courses da programs na musamman a fannin digital marketing, e-commerce, da entrepreneurship, inda ya kara kwarewa sosai a harkar internet.

A wani bangare, Sunusi Danjuma ya taba shiga harkar siyasa. Wanda a yanzu ya ja baya da ita gabadaya. Sa’annan magoyin bayan club din manchester united ne wanda yake bayyana ra’ayinsa koda yaushe game da kwallon kafa.

Shigarsa Duniyar Cryptocurrency Da Web3

Sunusi ya fara harkar cryptocurrency tun shekarar 2016, lokacin da fasahar blockchain ke samun karbuwa a hankali a duniya. A farkon shigar tasa, sha’awar decentralization ne ta kara masa ra’ayin harkar, domin kana da ikon samun kudi da kuma sarrafa shi ba tare da ikon wata hukuma ko gwamnati ba.

Daga nan sai ya cigaba da habaka har ya zama fitaccen mai ba da shawara, mai nazari, kuma mai talla (marketer) a fagen Web3.

A 2020, ya fara wallafa bayanai a Facebook kan crypto. Wanda hakan ta zamto wata hanya da matasa ke koyon abubuwa daga wurinsa kyauta. Bayan haka ya kafa community a waurare irinsu WhatsApp, sannan a Febrairy 2021, ya kirkiro da SCTv Africa wacce take nufin Sunusi Crypto TV Africa wanda ke aiki a matsayin dandalin ilmantarwa kan cryptocurrency da blockchain ga al’ummar Afirca.

Sunusi Danjuma Ali’s Net Worth

Har izuwa yanzu Simas Academy bata tantance adadin abinda Sunusi Danjuma Ali ya mallaka ba, sakamakon yadda tsarin kasuwancinsa yake. Amma a hasashe mun gano cewa matashin yana da a kalla kadarar sama da $90,000, wato Naira 140M.

Kalubalen Da Ya Fuskanta

Kamar yadda kowanne gwanin nasara yake fuskanta, shima Sunusi Danjuma Ali ya gamu da nasa kalubale da dama, wadanda suka hada da:

  • Rashin wadatattun kayan aiki a farkon rayuwarsa.
  • Cikas daga rashin fahimtar abokai da yan uwa game da al’amuran internet da karatunsa.
  • Kalubale ta bangaren tattalin arziki da ya kan hana matasa cimma burinsu.
  • Matsalolin da ya ringa fuskanta daga kananun abokan kasuwanci masu adawa dashi.

Sai dai, ya ci gaba da dagewa da jajircewa har ya izuwa wannan matakin da yake.

Nasarorin Da Ya Cimma

Mining & Airdrop Farming

  • Sunusi ya yi fice a harkar mining da airdrop farming. A 2023, ya shiga cikin top7 na masu mining sama da miliyan 4 a ICE Blockchain (ice_blockchain).
  • A wani mining campaign daban, ya kuma shiga cikin top 3 daga cikin mutane 1.97M participants, wannan yana tabbatar da tasirinsa da kuma community leadership.

Ambassador & Collaborations

  • A 2024, ya zama Bitget Global Ambassador, inda ya taimaka wajen tallata fasalin su na copy-trading.
  • Sa’annan yayi partnership da shahararrun platforms ta hanyar reviews da tallace-tallace, ciki har da:
    • Roqqu
    • Quidax
    • Busha
    • Xend Finance
  • Yana yawan magana kan cNGN (Compliant Naira), Naira stablecoin da ke aiki a blockchains daban-daban.

Public Speaking, Media & Community

Sanusi At Roqqu Event
Sunusi Danjuma Ali @ Roqqu Event
  • A May 2025, Sunusi ya gabatar da jawabi a babban taron da The Orange Block suka shirya a Kano, inda dubban matasa suka halarta kuma ya jawo hankalin su kan damar da Web3 ke bayarwa.
  • A June 2025, ya bayyana a TECH FM Radio, inda ya yi bayani kan yadda crypto ke sauya tsarin kudin duniya.
  • A Twitter Spaces, ya sha tattaunawa da manyan masana irin su CreptoSolutions da UkashatBalaCCII, musamman wajen nazari kan airdrop strategies kamar KaitoAI, Wallchain, da CookieDotFun.
  • Shi ne mutumin da ya fara bayyana wa matasan Arewa harkar DEX Trading a kyauta, abin da ya baiwa matasa dama su samu ilimi mai zurfi kan decentralized exchanges.

Wasu Daga Cikin Ayyukan Da Yaci Gaba

Har izuwa yanzu Sunusi na ci gaba da:

  • Samar da contents na koyarwa (musamman videos).
  • Shirya Twitter Spaces kan sabbin airdrops da DeFi projects.
  • Tallata cNGN tare da Roqqu Wallet.
  • Halartar ayyuka da tarurruka kan halal trading a Musulunci da Web3 opportunities ga matasa.
  • Karin tarurruka da events musamman ta SCtv
  • Shirye-shiryen koyarwa a harsuna daban-daban a Africa (Ba iya Hausa ba)
  • Hadin gwiwa da manyan kamfanoni da cibiyoyi a fagen fasaha da crypto, watakila Simas Academy tana ciki?

Darasi Daga Rayuwarsa

Tarihin Sunusi Danjuma Ali ya nuna mana cewa nasara bata zuwa cikin sauki. Tabbas Nasara tana bukatar hakuri, jajircewa, da kuma imani a kan abinda kake yi. Yana koyar da cewa koda mutum ya fito daga yanayin kalubale, idan ya dage ya tsaya zai iya cimma duk wani buri da yake dashi. Dama kuma Allah da kansa ya bayyana mana cewa dole zai jarabce mu da kalubale kafin muyi nasara a nan gidan duniya da lahira baki daya.

A Simas Academy, muna daukan irin wannan labari a matsayin darasi ga matasa da al’umma baki daya. Kar ka daina mafarki muddin a kan hanya yake, kar ka daina yin aiki a kan mafarkin saboda mutane suna maka kallon banza. Kaje ka duba tarihin wadanda sukayi nasara attajiran duniya, karon farko dariya ake yi musu.

Idan ka gwada ta wata hanyar bata yi ba, sai ka sake canjawa. Sa’annan Fasaha da internet sune zamani, a nan ne kake da cikakken yancin abinda kakeson yi, don haka internet na da ikon canza rayuwar kowa, kar kayi wasa da ita.

Yana da Kyakkyawan akid domin a dukkan shafukansa na sada zumunta, ya fi amfani da kalmar “Alhamdulillah” a koda yaushe.

Sa’annan bashida VIP Paid Classes, tun daga 2022, ya kuduri aniyar koyar da ilimin crypto kyauta ta hanyar YouTube dinsa. Duk wanda yace zai karbi kudi ya koya masa to tabbas Scammer ne domin baya haka. Baya sayan tokens daga hannun mutane, baya karban kudi saboda mentorship ko wani class, sa’annan Sunusi ya tabbatar da cewa duk wani abinda ya kasance zai karbi kudi ne daga hannun mutane baya yinsa, saboda haka a kiyeye.

Social Media & Community Handles

Saboda tabbatarwa, wadannan sune asalin (legit) Shafukan sada zumuntar sa:

Tambayoyin Da Zaka Iya Yi Game Da Sunusi Danjuma Ali

Wanene Sunusi Danjuma Ali?

Sunusi Danjuma Ali dan kasuwa ne daga Minjibir, Kano, Nigeria, wanda ya yi fice a harkokin fasaha da kasuwanci na zamani. An san shi da kwazon sa wajen kirkirar sabbin hanyoyin kasuwanci a yanar gizo da kuma taimakawa matasa wajen shiga harkar crypto.

Shin Sunusi Danjuma Ali Yana Da Aure?

Eh, Sunusi Danjuma Ali ya yi aure kuma yana da iyali. Yana yawan bayyana yadda goyon bayan iyalinsa ya kasance muhimmin sashi a nasarorin da ya samu a rayuwa.

A Ina Aka Haifi Sunusi Danjuma Ali?

An haifi Sunusi A garin Minjibir dake Jahar Kanon Nigeria.

Menene Asalin Karatunsa?

Ya yi karatunsa a Kano inda ya samu ilimi na boko, arabic da na fasaha. Daga baya ya nemi kwarewa a bangaren kasuwanci da fasahar zamani, abin da ya kara ba shi damar shiga harkokin duniya.

Ta Yaya Ya Fara Harkar Kasuwanci?

Ya fara ne da kananan jari, farko yana samun kudade a sana’arsa ta zahiri, daga nan ya fara zuba kudadensa a kasuwancin yanar gizo. Yaci gaba da samun gogewa har ya zama jagora ga matasa.

Menene Manyan Kalubalen Da Ya Fuskanta?

Kalubalen farko da ya fuskanta sun hada da rashin goyon baya da kuma karancin jari. Amma ta hanyar juriya da kwazo, ya yi amfani da duk wata dama da ta bayyana a gabansa.

Wane Tasiri Ya Yi Ga Al’umma?

Sanusi Danjuma Ali ya ba da gudummawa wajen wayar da kan matasa game da ilimin crypto. Sanadiyyarsa mutane da dama sun samu saukin shiga harkar crypto saboda ilimin da yake basu.

Wadanne Nasarori Ne Ya Cimma?

Ya kafa kamfanoni masu zaman kansu da suka shahara a fagen fasaha da kasuwanci. Haka kuma, ya samu yabo daga kungiyoyi da dama saboda irin gudummawar da yake bayarwa al’umma.

Me Yasa Ya Shahara A Najeriya Da Waje?

Sunusi Danjuma Ali ya shahara ne saboda hazakarsa wajen amfani da sabbin fasahohi da kirkirar hanyoyin samun kudi. Har ila yau, kasancewarsa mutum mai bayar da tallafi da shawarwari ya kara masa suna gida da waje.

Da Gaske Ne Sunusi Danjuma Ali Yana Bumburutu?

A’a, Sunusi baya bumburutu, wato saya da sayar da coins kai tsaye a hannun mutane. Duk wanda ya bayyana maka da sunan yana sayan coins to tabbas scammer ne, ka guje shi.

Bayan SCTv Africa Da Akwai Wata Kamfani Da Sunusi Yake Da Ita?

A halin yanzu babu, amma muna sa ran nan gaba matashin mai sha’awar kasuwancin zamani ya iya bude wata kamfani ta bangaren Technology.

Related Posts On Simas Academy