Blog
A duniyar yau, internet ya sauya yadda ake rayuwa, ya ba da damarmaki masu yawa na samun kudi wadanda ba dole sai mutum yaje yayi aiki a waje ba. A Zamanin nan da akwai mutane da yawa da suke aikin aikin ofis daga gida ta hanyar amfani da internet. Idan kana neman yadda ake samun kudi a internet, to ka tsaya ka karanta wannan shafin kuma ka fahimta.
Domin a wannan shafin munyi yi bincike kan hanyoyi guda goma sha daya (11) da ake samun kudi a online. Sa’annan munyi cikakken bayani kan yadda kaima zaka fara.
Kasuwancin Affiliate Marketing
Affiliate marketing daya ne daga cikin manyan kasuwanci a online, wanda za ka iya samun kudi ta hanyar tallata kayan wasu kana samun commission. Idan mutum ya sayi abu ta hanyar link dinka (Affiliate Link, ko referral link), zaka samu kaso daga cikin kudin. Wannan na daya daga cikin manyan kasuwancin da ake samun millions of Naira dasu a Nigeria.
Misali; a daya daga cikin manyan shafukan da ake affiliate shine Amazon, inda zaka je kayi register dasu (Amazon Associates) sai ka dauki link na kayan da kakeso ka tallata (Ka tabbata kana tallata abinda ya karbe ka). Haka zalika da akwai wasu stores, ko platforms kamar hosting companies da suke bayar da commission mai yawa.
Yadda Ake Fara Affiliate Marketing:
- Da farko, Ka zabi shahararren store kamar Amazon Associates, Jumia Affiliate, Selar, ko ClickBank sa’annan kayi register dasu.
- Na biyu kuma ka hada Website ko YouTube channel don yin review na kayayyaki (Ka janyo mutane su kalli kayayyakin domin su saya).
- Talla da promotions, idan da hali ka ringa hadawa da abinda zai ja hankalin mutane su sayi kayayyakin da kake tallatawa.
Shi wannan kasuwancin, Ba dole sai kana da kayayyaki a hannunka ba, A’a. Zuwa zakayi ka nemi kayan da mutane suke so kana tallata musu kai tsaye kana samun rabonka wato commission.
Blogging
Idan kana da sha’awar posting, kana da abinda idan ka rubuta mutane zasu karanta (Labarai, Litattafai, ko wasu sirruka) to wannan harkar ta Blogging taka ce. Blogging na daya daga cikin hanyoyin samun kudi mafi inganci a internet musamman ma nan Nigeria. Zaka iya kirkirar blog a kan kowanne fanni kamar lafiya, fasaha, kasuwanci, ko nishadi domin ka ringa samun kudi daga wadanda suke karantawa (visitors).
Yadda Ake Fara Kasuwancin Blogging:
- Ka fara da zaben wani fanni da kake da sha’awa kuma kana da ilimi a kansa.
- Sa’annan ka bude website ko ta hanyar amfani da Blogger ko WordPress (Muna da courses da zasu taimaka kayi wannan)
- Ka fara saka abubuwa masu amfani da zasu sanya mutane su ringa zuwa shafin, musamman a koda yaushe ka wallafa sabon abu (post, video, photo, ya danganta da abinda website din naka yake tafiya a kai).
- Kayi applying na monetization ta hanyar amfani da Google AdSense, AdsTerra, Monetag, sponsored Posts, ko Affiliate Marketing.
Dadin Blogging shine yana iya kawo kudi na tsawon lokaci in dai ka lura da website dinka da kyau kuma ka dauke shi da mutunci, zaka samu yanzu haka da akwai bloggers dinda suke rike da website dinsu fiye da shekaru goma kuma har izuwa yanzu suna samun revenue (kudi).
Ga wannan course din da zai taimaka maka da sirrin yadda zaka bude website kyauta har a fara biyan ka.
Kasuwancin Dropshipping
Dropshipping wata hanya ce mai sauki da mutum yake samun damar siyar da kayayyaki ba tare da ya mallake su ba. A wannan kasuwancin, kai ba ka da kayan; kawai zaka nemi ingantaccen store (online irinsu Temu, AliBaba, Jumia, Konga da Sauransu) sai ka saya a arha. Daga nan kaikuma ka sayar ga wanda yake so (online).
Dropshipping kamar kamar Affiliate Marketing Yake, kana bukatar neman trending products da ake yayi a niche da kake. Daga nan sai ka nemi store din da suke sayar da kayayyakinsu a arha, sai kazo ka tallata (Inma ta hanyar content, ko yadawa target audince dinka). Duk wanda yake bukata
Yadda Ake Farawa:
- Zaka nemi platform da zaka yi amfani dashi (website) kamar Shopify ko WooCommerce, Ko kuma ka biya Web Developers su kirkiro maka maka.
- Daga na ka nemo store da zaka sayi kayan, kamar AliExpress, Temu, Jumia, Amazon, ko wani wajen (Ka tabbatar suna da sauki).
- Ka gyara wannan platform din yayi kyau, sa’annan ka saka wasu features masu kyau (Tsarin email marketing, Good UX/UI, SEO).
- Daga nan ka fara tallatawa a social media, ko kuma ta hanyar bada Ads.
Wannan kasuwancin ba’a fiye yinsa ba, musamman ma a nan Nigeria sakamakon samun customers yana da wahala.
Freelancing
Freelancing na nufin yiwa wani aiki (company ko individual) ta yanar gizo sa’annan su biya ka kudin aikin. Wannan kasuwancin na daya daga cikin manyan kasuwancin da suka shahara a duniya kuma yana bada damar aiki daga gida. Akwai ayyuka da ake daukar mutum yayi kamar rubuce-rubuce, fassara, zane-zane, programming, da dai sauransu.
Yadda Ake Freelancing:
- Da farko ka tabbatar kana da wata kwarewa da ake bukata. Editing, Programming, Translating, Voice, content creation, da sauransu.
- Sai kayi rijista a shafukan freelancing kamar Fiverr, Upwork, Simas Jobs ko PeoplePerHour.
- Daga nan sai ka sanya bayanan ayyukan da kake iya yi da kuma farashin da za’a biya ka (Ka duba kaga top performers sa’annan ka koya daga garesu).
- Ka ringa neman connection da mutane su san aikinka da kwarewarka, Musamman a shafukan sada zumunta, X, LinkedIn da sauransu.
Shi freelancing ana iya samun kudi masu yawa idan kana da skill kuma ka iya aiki mai kyau, domin zaka iya samun a baka aiki na din-din-din wato Full-time job.
YouTube
Ka taba tambayar kanka meyasa directocin fina-finai da producers suke kashe kudi masu yawa su hada film sa’annan su dora a YouTube? Idan mukayi duba da manyan industries dinmu na Nigeria wato Kannywood da Nollywood zamu ga suna saka fina-finansu kai tsaye a YouTube.
Musamman ma Kannywood da suka daina saka film a ko ina sama da YouTube. To ka sa irin alherin da suke samu daga YouTube din kuwa? Ba sai an fada maka ba. Dandalin YouTube na daya daga cikin hanyoyin samun kudi ta hanyar kirkirar bidiyoyi masu jan hankali kaima zaka ringa samun kudade ta internet idan kana da idea da abinda zaka ringa sakawa a YouTube.
Yadda Ake Fara YouTube:
- Ka fara gano fannin da kake da kwarewa kuma kake da sha’awa a kai (kamar koyarwa, nishadi, ko ilimi).
- Ka bude channel dinka mai kyau tare da tsara shi da bidiyons masu inganci da zai amfanar da mutane.
- Saura subscribers da watch time hours, daga nan kayi applying na Google AdSense a fara biyan ka.
Facebook Content Creation
Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin da za ka iya amfani da shi don samun kudi. Duk da cewa hanya ce mai matukar wahala sakamakon yadda dokokin Meta suke da tsauri da kuma yadda mutane sukayi yawa, amma idan kana hada contents masu inganci da mutane suke so, to tabbas zaka ringa samun kudi daga Facebook.
Yadda Ake Samu Daga Facebook:
- Zaka fara Gina shafi ko profile (professionalmode) dinka na Facebook tare da saka contents masu jan hankali (No copyright, banda batsa ko cin zarafin wani, ko abubuwan tada hankali).
- Kayi kokari ka ta followers ta hanyar posting da bidiyoyi, rubuce-rubuce, da hotuna masu jan hankali sossai, kuma akai-akai.
- Daga nan idan ka samu 10,000 followers kuma baka saba doka ba sai kayi applying na Monetization.
Online Courses
Online Course hanya ce ta koyarwa ta yanar gizo inda kwararru ke kirkirar darussa a kan wani fanni, sannan dalibai su koya daga ko ina cikin sauki. Ana iya amfani da bidiyoyi, audio, hotuna, rubutu, da tambayoyi wajen koyarwa (Kamar yadda ake yi a Simas Academy, Udemy, Flowdiary, da sauran makarantun internet).
Kai tsaye idan kana da wata kwarewa wanda ka tabbatar zata taimaki mutane, to zaka iya hada course kuma kayi amfani da wadannan makarantu na internet ka wallafa course dinka. Daga nan duk wanda ya saya zaka ringa samun kudin kai tsaye a account dinka.
Yadda Ake Samun Kudi Da Online Courses:
- Da farko dole ya kasance kana da ilimin da zaka koyar din, kuma ka tabbata mutane suna bukatar shi zasu iya biya.
- Na biyu, ka hada course din yadda dalibai zasu fahimce shi ba tare da sun sha wahala ba.
- Na uku neman platforms (online institutes) da suke bada damar masu kwarewa su wallafa courses dinsu don samun kudi misali: Simas Academy, Udemy, Teachable, ko YouTube Membership.
Wannan na daya daga cikin kasuwancin da yake bada riba, musamman idan kana da kwarewa ta musamman to zaka ringa tara dalibai kana taimakon su da abinda ka sani.
Social Media Marketing (SMM)
Social Media Marketing hanya ce ta amfani da Facebook, Instagram, TikTok, Twitter, ko YouTube don tallata kaya, services, ko wani company (brand), a wani bangaren harda tallata mutum (musamman dan siyasa). Ana amfani da posts, bidiyoyi, ko talla (ads), don jan hankalin mutane. Idan kana da sha’awar social media, zaka iya samun kudi ta hanyar tallata brands ko kula da shafukan social media dinsu.
Yadda Zaka Fara Kasuwancin:
- Ka fara koyon digital marketing da social media management.
- Ke nemi brands da ke bukatar tallatawa, ko kuma ka nemi companies da basu dashi ka basu shawari tare da nuna musu aikinka.
- Daga nan kaci gaba da aiki da mutane daban-daban saboda ka ringa samun connection.
Cryptocurrency
Cryptocurrency kudi ne na zamani da ake amfani da shi ba tare da sa hannun banki, hukuma ko gwamnati ba. Misalan shahararrun crypto sun hada da Bitcoin, Ethereum, da BNB. Ana iya samun kudi daga crypto ta hanyoyi daban-daban. Wanda idan mun duba zamu ga wasu da yawa sun samu arzikinsu ne ta hanyar Kasuwancin Crypto, wasu Airdrop, Wasu Mining, Wasu Trading da sauransu.
Yadda Ake Samun Kudi Da Cryptocurrency:
- Mining Hakar crypto ce inda ake amfani da computer masu karfi wajen mining na coins.
- Trading shine siye da sayar da coins ko tokens na crypto don samun riba.
- Sai kuma Holding (HODL) na coin na dogon lokaci har sai darajarsa ta karu (CZ Binance yace idan kanason nasara a harkar crypto, to kayi holding)
- Shikuma Staking na nufin ajiye crypto a cikin wallets na dan wani lokaci don samun riba.
- Airdrops kuma samun crypto kyauta daga wasu kamfanoni, misali Pi Network, Sidra, Dogs, Paws da sauransu.
Graphic Design
Graphic Design sana’a ce ta musamman da ake samun na kashewa daga internet, Inda mutum zai ringa aikin hada hotuna masu kyau na talla, social media, websites, ko na kamfani a biya shi. Ana amfani da software irnsu Canva, Photoshop, Pixellab (Mobile) CorelDRAW da sauransu don yin aikin.
Yadda Ake Graphic Design:
- Ka fara koyon design din daga wanda ya kware ko kayi amfani da YouTube, Simas Academy, Flowdiary, ko Udemy a koya maka.
- Ka kirkiri Portfolio ta yadda zaka ringa nuna ayyukanka da zai sa mutane su ringa baka aiki saboda iyawar ka.
- Zaka iya Freelancing ta hanyar yin rijista a shafukan Fiverr, Simas Jobs, Upwork, ko 99Designs.
- Idan kana bukatar samun customers, ka kulla alaka da mutane sossai a social media ka kuma ringa basu offer.
11. Forex Trading
Forex Trading daya ce daga cikin manyan hanoyiyin da ake samun kudi ta internet. Inda idan muka duba zamu ga cewa da akwai matasa da yawa a Nigeria wadanda suka samu arziki ta wannan hanya. Forex hanya ce ta ciniki da musayar kudaden kasashe daban-daban don samun riba. Ana saye da sayar da kudi kamar USD, EUR, GBP, da JPY bisa ga hauhawar farashinsu ko faduwa. Ana iya amfani da pairs daban-daban wajen yin trading din, ciki harda crypto coins irinsu Bitcoin.
Kammalawa
Samun kudi a intanet yana bukatar natsuwa, juriya, da kuma dabaru wato strategies. Ka fara dubawa wace hanya ce ta fi baka sha’awa? Sa’annan kayi dogon bincike daga malaman ka (bisa ga addininka) ka tabbatar da ingancinsa (Haram/Halal) sa’annan ka fara. Bugu da kari idan kana da wata tambaya ko karin bayani kai tsaye kayi ta comment.
[…] Karanta: Yadda Ake Samun Kudi A Online. […]
[…] na daya daga cikin kafofin da mutane da dama ke amfani da shi wajen samun kudi daga internet, ta hanyar creating na bidiyoyi masu amfani ko nishadi. Ko da kuwa ba ka da kawarewa ko kayan aiki […]
Allah yasa da alkhairi muna gdy,amma taya ake tsara blog yaxama yanada sauqin downloading.
Blog na din downloading kake magana a kai?
Good
Message aslm
Hello good day