Have a question?
Message sent Close

FAQs

Find Answers To All Your Questions About Simas Academy – From Courses Access, Payments, Account Setup, Certification, To Learning Support. Everything You Need To Know Before And After Enrolling, All In One Place. If You Have Further Question About Simas Academy FAQs Let Us Know.

Menene Simas Academy?

Simas Academy wata makarantar koyar da sana’o’in zamani ce ta yanar gizo da ke koyar da digital marketing, sana’ar intanet, da dabarun kasuwanci na zamani. An kafa ta domin taimakawa matasa, mata, dalibai da masu neman karin kudin shiga ta hanyar ilimi mai amfani da za a iya amfani da shi kai tsaye.

Menene Abubuwan Da Simas Academy Ke Koyarwa?

Simas Academy tana koyar da fannoni kamar: Digital Marketing, Blogging, Website Creation, Cryptocurrency, Graphic Design, Video Editing, Content Creation, da Online Business Models. Duk darussan suna da sauki kuma ana koyar da su cikin harshen da kowa zai fahimta.

Shin Simas Academy Yana Koyar Da Aiki Ne Ko Karatu Ne Kawai?

Aiki da karatu duka ana koyarwa. Wannan na nufin ba wai karatu kawai za ka yi ba, za ka koyi yadda zaka aiwatar da abin da aka koya domin samun kudi daga sana’ar. Simas Academy tana koyar da practical skills da za ka iya amfani da su kai tsaye.

Shin Simas Academy Cikin Harshen Hausa Ne Ko Turanci?

Simas Academy tana samar da darussa ne cikin harshen Hausa da kuma Turanci. Wannan yana saukaka fahimta musamman ga wadanda ba su da kwarewa sosai da Turanci. Dalibai za su iya zaɓar harshen da ya fi sauki gare su.

Zan Iya Koyon Sana’ar Digital Marketing A Simas Academy?

Eh, Simas Academy tana da cikakken course akan Digital Marketing. Za ka koyi abubuwa kamar Social Media Marketing, Email Marketing, SEO, da yadda zaka tallata kayanka ko ayyukanka ta intanet domin samun kudi.

Shin Ana Samun Certificate Bayan Gama Course A Simas Academy?

Eh, bayan kammala kowanne course a Simas Academy, ana ba dalibi certificate na kammalawa wanda ke nuna cewa ka koyi wannan sana’a. Wannan certificate na iya taimakawa wajen samun aiki ko gina sunanka a sana’ar da ka koya.

Tsawon Wane Lokaci Ake Dauka Kafin A Kammala Karatu?

Lokacin karatu ya danganta bisa ga course din da ka zaba. Wasu courses na iya daukar sati biyu, wasu kuma wata daya zuwa biyu. Duk da haka, kana iya karatu a lokacin da kake so saboda tsarin yana da sauki (self-paced). Amma ana so a lokacin da kakae karatun kana implementing na abinda kake fahimta.

Shin Simas Academy Yana Da Mobile App?

A halin yanzu, Simas Academy tana aiki ne a yanar gizo ta hanyar shafin su. Duk da haka, ana iya samun saukin amfani da courses din ta hanyar amfani da waya ko computer. A nan gaba, akwai shirin kirkiro mobile app domin saukaka amfani.

Ta Yaya Zanyi Registration A Simas Academy?

Zaka iya yin rijista kai tsaye ta hanyar ziyartar https://simasacademy.com.ng, danna “Register” ko “Join Now”, sannan ka cike bayanan da ake bukata, mafi sauki da zaka iya register da Google dinka ko X account. Bayan haka za a tura maka cikakken bayani akan yadda zaka fara karatu.

Yaya Zan Samu FREE Courses Daga Simas Academy?

Simas Academy tana da FREE courses da kuma na kudi. Akwai manyan darussa masu zurfi da ake biya, amma akwai courses na kyauta domin taimakawa masu karamin karfi su fara samun ilimin da zasu iya yin wani abu. Mutum na iya samun scholarship ko wani tallafi da wasu kungiyoyi suke bayarwa ga Simas Academy.

Ina Zan Ga Jerin Courses Dake Simas Academy?

Zaka iya duba jerin courses na Simas Academy ta hanyar ziyartar shafin su sannan ka shiga bangaren “Courses” ko “All Courses” domin ganin dukkanin darussa da suke akwai.

Waye Zai Amfana Da Simas Academy?

Matasa, dalibai, housewives, masu neman aikin yi, da masu kasuwanci da suke son koyon yadda za su bunkasa harkokinsu ta intanet, dukkansu za su amfana daga Simas Academy.

Shin Ana Koyar Da Blogging A Simas Academy?

Tabbas da akwai cikakkun courses na blogging a Simas Academy dake koyar da shi for Business, and for money. Sa’annan harma da mentorship program ga wadanda suke cikin harkar.

Zan Iya Koyon Hanyoyin Samun Kuɗi A Intanet A Simas Academy?

Tabbas! Hanyoyin samun kudi a online su ne jigon koyarwar Simas Academy. Akwai darussa da ke koyar da hanyoyi irin su blogging, YouTube, TikTok, freelancing, da kuma kasuwancin crypto da forex.

Shin Ana Koyar Da Crypto A Simas Academy?

Simas academy bata koyar da crypto kai tsaye, amma tana partnership da kwararrun masu ilimin crypto don koyar da wadanda suke da bukata cikin sauki.

Idan Na Kammala Karatu Zan Iya Samun Aiki?

Simas Academy tana koyar da sana’o’in da zaka iya amfani da su kai tsaye don samun kudi, ko dai ta hanyar freelancing, kasuwanci, ko kirkirar abun a online. Yayin da ba lallai ne su baka aiki kai tsaye ba, abinda zaka koya zai baka damar kirkiro ayyukan kanka ko samun aiki a online platforms, samun aiki a ko ina, saboda kana da skill.

Shin Simas Academy Yana Da Community Na Dalibai?

Eh! Simas Academy tana da babban community mai suna African Tech Forum, inda dalibai da malamai ke tattaunawa, taimakon juna. Wannan yana taimakawa wajen karfafa hadin kai da ci gaba da koyo tsakanin mutane.

Ta Yaya Zanyi Hulda Da Malaman Simas Academy?

Zaka iya hulda da malamai ta hanyar group din community, ko ta hanyar tambaya a cikin kowane course. Hakanan akwai wasu courses da ke bada damar live Q&A ko group mentoring.

Ta Yaya Simas Academy Ke Taimakawa Matasa Da Mata Marasa Aiki?

Ta hanyar koyar da skills masu amfani kamar digital marketing, YouTube, da blogging, Simas Academy na ba wa matasa da mata damar koyo daga gida ba tare da kashe kudi mai yawa ba, har su iya fara kasuwanci ko aikin online.

Shin Courses Na Simas Academy Zasu Iya Taimaka Min Nemi Aiki?

Eh kwarai! Idan ka kammala karatu kuma ka samu certificate, zaka iya amfani da shaidar wajen neman aiki, musamman a fannonin da ke bukatar skills kamar content writing, marketing, design, da sauransu.

Zan Iya Tambayar Malami Kai Tsaye Bayan Na Kammala Karatun Course?

Tabbas. Idan kana da tambaya bayan ka koyi course, zaka iya turo tambayarka a cikin platform ko group na community domin a taimake ka. Malamai da members na kusa suna nan don amsa tambayoyi.

Shin Simas Academy Na Yanar Gizo Ne Kawai Ko Suna Da Ofishi?

Simas Academy na aiki ne a yanar gizo gabadaya saboda ya saukakawa mutane masu neman digital marketing skills da sauki. A halin yanzu babu ofishi ko makaranta na zahiri, amma ana shirin fadada hakan a nan gaba.

Dalibai Nawa Ne Suka Kammala Karatu Daga Simas Academy?

A halin yanzu, daruruwan dalibai ne suka koyi skills daga Simas Academy, ciki har da wadanda suka fara aiki da abinda suka koya. Sa’annan yawan dalibai yana karuwa kullum.

Simas Academy Da Flowdiary Duka Daya Ne?

A’a, Simas Academy na da banbanci da Flowdiary, sa’annan suna da banbancin tsare-tsare. Amma sai dai dukkansu suna taimakawa wajen koyawa mutane ilimin Digital Marketing Skills.

Yaya Simas Academy Ke Taimakawa Masu Online Business?

Ta hanyar koyar da digital marketing, content creation, da business strategy, Simas Academy na taimakawa masu kasuwanci su bunkasa harkokinsu a online. Hakanan, akwai topics da ke bayani kan yadda za a sayar da kaya ko services ta internet.

Ina Zan Iya Bi Don Samun Sabbin Darussa Da Labarai Daga Simas Academy?

Zaka iya ziyartar shafin yanar gizo na Simas Academy a https://simasacademy.com.ng ko kuma ka shiga African Tech Forum domin samun updates na sabbin courses, labarai, da kuma dama. Zaka iya zuwa social media handles dinsu ka kasance tare da community.

Me Yasa Ya Kamata Na Zabi Simas Academy Akan Wasu Online Schools?

Saboda Simas Academy tana koyarwa cikin harshen Hausa da Turanci, tana cikin sauki, tana da community mai karfi, kuma tana mayar da hankali wajen koyar da ilimin da ake samun kudi dasu, kasuwanci da kuma skills da ake gina career dasu. Ba iya karatu na theory kawai ba, harda practical knowledge and experience.