
- Description
- Curriculum
- FAQ
- Reviews
- Grade
Wannan Course Din Zai Koyar Da Kai Yadda Za Ka Hada Website Ta Hanyar Amfani Da Ilimin WordPress, Daga Mataki Na Farko Har Zuwa Matakin Da Za Ka Iya Gina Shafin Yanar Gizo Naka Kai Tsaye A Kan CPanel (Hosting) Ba Tare Da Dogaro Da Kowa Ba.
A Wannan Course Din Za Ka Fahimci Menene WordPress, Siffofinsa, Wandanda Ke Amfani Da Shi, Da Dalilin Da Ya Sa Kai Ma Ya Kamata Ka Yi Amfani Da Shi. Haka Kuma, Za Ka Koyi Yadda Ake Amfani Da Localhost (XAMPP) Idan Kana Da Computer Don Gwadawa Kafin Ka Tura Shafin Ka Kai Tsaye A Kan Hosting.
An Tsara Wannan Course Ne Cikin Harshen Hausa Kai Tsaye. Babu Wasu Kalaman Da Zasu Wahalar Da Kai. Kuma Zai Taimaka Maka Kai Tsaye, Ko Mace Ce Dake Gida, Ko Mai Sha’awar Fara Kasuwanci A Internet Ta Hanyar Gina Shafukan Yanar Gizo.
🧠 Me Za Ka Koya A Wannan Course Din?
-
Fahimtar WordPress CMS
-
Siffofin WordPress Da Dalilin Amfani Da Shi
-
Manyan Kamfanonin Dake Amfani Da WordPress A Duniya
-
Yadda Za Ka Yi Amfani Da Localhost/XAMPP A Computer
-
Yadda Ake Dora WordPress A Kan Hosting Ta CPanel
-
Yadda Ake Amfani Da Themes Da Plugins
-
Yadda Ake Tsara Shafuka Mai Kyau (Page & Post Creation)
-
Yadda Ake Saka Hotuna, Bidiyo, Da Documents
-
Yadda Ake Gyara Menus, Widgets, Da Shafuka Masu Tsari
-
Yadda Ake Tsara Basic SEO
-
Tsare-Tsaren Kare Website Daga Hare-Haren Internet
💡 Wannan Course Din Zai Taimaka Wa:
-
Matasa Masu Sha’awar Koyo Da Samun Sana’a Ta Internet
-
Matan Gida Masu Neman Hanyar Samun Kudi Daga Gida
-
Masu Sha’awar Kafa Blog, Shagon ECommerce, Ko Shafin Kamfani
-
Duk Wanda Yake Da Waya Mai Kyau Ko Computer Kuma Yana Son Shiga Harkar
-
1Menene WordPress Da Dalilin Shahararsa
-
2Muhimman Abubuwan Da WordPress Ke Da Su
-
3Wadanda Ke Amfani Da WordPress CMS
-
4Dalilin Da Ya Sa Ya Kamata Ka Yi Amfani Da WordPress
-
5Bambanci Tsakanin WordPress.com Da WordPress.org
-
6Yadda WordPress Ke Aiki
-
7Module 1 Glossary
-
8Gwajin Fahimtar WordPress (I)Wannan Gwaji Ne Da Zai Taimaka Maka Wajen Tantance Irin Fahimtar Da Ka Samu Game Da WordPress, Matakin Farko A Darasin Module (I) Na WordPress Web Development [Hausa].