Get Our Free New Course >> Artificial Intelligence Program.
HomeNewsSimas Academy Ta Kaddamar Da Course Din Video Content Creation

Simas Academy Ta Kaddamar Da Course Din Video Content Creation

  • January 27, 2026
Sabon Course Na Video Content Creation

Zamanin nan zamanin Content Creators ne, inda mutane ke amfani da kafofin sada zumunta kamar Facebook, TikTok, YouTube da sauransu domin koyarwa, nishadi da kuma samun kuÉ—i. A wani babban mataki na bunkasa ilimin zamani a Arewacin Nigeria da ma Africa baki daya, Simas Academy ta sanar da kaddamar da sabonta kuma farkon course dinta mai suna Video Content Creation Course In Hausa.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan wani dogon shiri na pre-launch da aka fara tun ranar 24 ga Disamba, 2025, inda aka gwada tsarin course din, aka tattara ra’ayoyin al’umma, sannan aka inganta abubuwan da za a koyar domin su dace da bukatun masu koyo.

Dalilin Kaddamar Da Course Din

Sabon Course Na Video Content Creation

A baya, yawancin ‘yan Najeriya na ganin cewa samun kudi daga content creation abu ne mai wahala, musamman a Facebook, YouTube, da TikTok. Amma a yanzu abubuwa sun sauya. Facebook da wasu manyan platforms sun fara biyan yan Nigeria kudaden shiga ta hanyar revenue programs, reels, in-stream ads, da sauran hanyoyi.

Ba iya wannan ba, yan kasuwa yanzu a Nigeria sun fara wayewa da shiga internet wajen bunkasa kasuwancinsu. Don haka suke bukatar ilimin da zai basu damar kikiro video contents na kasuwancinsu, kamar adverts, products, da bayanai a kan kasuwancin.

Simas Academy ta fahimci wannan dama, kuma ta yanke shawarar kirkirar course na musamman da zai taimaka wa matasa, dalibai, ma’aikata, mata da maza, su koyi yadda za su shiga harkar Video Content Creation cikin tsari, ilimi da kwarewa.

Menene Video Content Creation Course?

Video Content Creation Course In Hausa wani cikakken shiri ne da aka tsara domin koyar da masu sha’awar content creation yadda za su zama kwararrun video content creators, ta hanyar amfani da wayar hannu (Android ko iPhone) ko computer.

Course din yana koyar da yadda ake kirkirar videos masu jan hankali da kuma masu yuwuwar zuwa viral, ba tare da wahala ko tsadar kayan aiki ba.

Abubuwan Da Ake Koyarwa A Cikin Course Din

A cikin wannan course, duk wanda yayi regsiter zai koyi:

  • Kirkirar Movie Recaps da bidiyon labari
  • Storytelling Videos masu jan hankali
  • Lyrics Videos
  • Voice Over Videos
  • AI Content Videos
  • Business Video Contents
  • Amfani da bidiyo wajen ilmantarwa da nishadi

Haka kuma, zaka koyi:

  • Gyaran bidiyo ta amfani da KineMaster da CapCut
  • Dabarun editing na zamani
  • Hanyoyin samun viral views a TikTok, Facebook, da sauran platforms
  • Yadda ake gina personal brand a social media

Abubuwan Da Ake Bukata Kafin Fara Course Din

Daya daga cikin abubuwan da suka sa wannan course ya zama na musamman shine saukinsa. Abubuwan da ake bukata sun hada da:

  • Wayar Android ko iPhone mai kyau, ko Computer
  • Apps na editing (KineMaster, CapCut)
  • Internet connection domin download da upload
  • Shirye-shiryen koyon ilimin da gaske (Bada lokaci)

Takardar Shaida (Certificate)

Bayan kammala course din, duk wanda da ya kammala karatu yadda ya dace zai samu takardar shaida (certificate) kyauta daga Simas Academy, wacce za ta nuna cewa ya kammala horo a fannin Video Content Creation.

Yadda Ake Samun Course Din

Masu sha’awar shiga wannan course za su iya:

Da zarar an yi register, za a ba É—alibi cikakken access na course din.

Hausa Video Content Creators Community

Domin kara inganta koyo da samar da ilimin da ya dace, duk wanda ya yi register zai samu access zuwa Video Content Creators Class na Simas Academy a Telegram. Mutum yana yin tambayoyi a kowane lokaci sa’annan Ana exchanging na ra’ayoyi da ideas.

Muhimmancin Course Din Ga Matasa Da Masu Sha’awa

Wannan course ba wai koyarwa kawai yake yi ba, zai buÉ—e maka kofa zuwa:

  • Samun kudi daga internet
  • Gina sana’arka ta kanka na zamani
  • Dogaro da kai ta hanyar amfani da ilimin
  • Da kuma karin samun damar shiga sahun content creators na duniya;

Daga karshe, kar kayi wasa da wannan damar da Simas Academy ta kawo maka, tun kafin lokacinka ya kure, tun kafin ayi nisa a bar ka, tun kafin ya girma, kayi kokari ka shige gaba! Wannan dama ce, domin ba iya koyarwa da kai za’ayi ba, har ma da bude maka wasu hanyoyi za’ayi.

Leave a Comment

Anthony Joshua, tsohon zakaran dambe na duniya wanda ya shahara a duk fadin duniya, ya shiga wani mummunan hatsarin mota...
Learn How To Check BVN Number Using A Code That Works Fast. A Complete Guide On Safe, Quick, And Reliable...
In a futuristic reflection on the rise of Artificial Super Intelligence (ASI), Nigerian tech thinker Aliyu Saidu Jauro has declared...
Who Are The Top Richest Crypto Traders In Africa? And The Richest Forex Traders In Africa? As We Dive In...