Blog
Sirrin Yadda Ake Samun Kudi A Facebook
- May 21, 2025
- Posted by: Joseph Micheal
- Category: Hausa

Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin da content creators suke bi wajen samun kudi a social media. A nan zaka karanta sirrin yadda ake samun kudi a Facebook. A baya, yan Nigeria basu da damar samun kudi kai tsaye daga Facebook saboda tsari na babban kamfaninsu Meta. Amma yanzu, lamarin ya canza, A shekarar 2024 zuwa 2025, Meta ta sanar da kawo tsarin monetization ga wasu kasashe ciki har da Nigeria da Ghana.
Amma fa, duk da cewa wannan damar, samun kudi daga Facebook ba yana nufin kawai ka saka bidiyo ko Reels ka fara samun kudi bane. A’a. Tsari ne da yake da dan wahala, shiyasa dole kana bukatar hakuri, kuma ya kasance kana iya creating na contents masu jan hankali. Shiyasa muka samar da course din Social Marketing da kuma Content Creation Course da zasu koya maka daga A-Z.
Yaya Ake Samun Kudi Daga Facebook?
Samun kudi a Facebook wato Monetization na nufin damar da masu content ke samu don Facebook ya biya su saboda abun da suke sakawa kamar bidiyo, Reels, ko posts a profiles dinsu. Hanyoyin samun kudi a Facebook suna da yawa, da akwai: In-Stream Ads (Talla cikin Bidiyo), Ads on Facebook Reels, Facebook Stars, Subscription, Sponsored Posts, Affiliate Marketing, Facebook Marketplace (Indirect Monetization).
Yadda Facebook Suke Biya
Facebook suna biya ne ta hanyar amfani da CPM model, wato cost per mille. Cost per mille na facebook shine abinda suke biyanka a kan kowane viewers dubu daya. Idan CPM Dinka ya kai dala 1, to kowane impressions guda 1,000 zaka samu $1, amma sai dai ba’a cika samun CPM mai yawa ba, Musamman a tier 3 countries irinsu Nigeria.
- Ad views: Adadin mutanen da suka kalli tallar.
- Video watch time: Tsawon lokacin da mutane suka kalli bidiyon.
- Retention rate: Shin mutane suna kallon bidiyon har karshe?
- Geographic location: Kasar da masu kallon suka fito (misali idan US ne ko UK sunfi fi biyan kudi fiye da Nigeria ko irinsu Ghana).
Bayani Kan Hanyoyin Samun Kudi Ta Facebook
In-Stream Ads (Talla Cikin Bidiyo)
Na farko, In-stream ads, tsarin da Facebook ke saka talla a cikin bidiyoyinka, musamman idan sun haura minti 1. Misali, bidiyo zai fara, sai talla ya bayyana kafin ko yayin da ake kallon sa. Idan kana da bidiyo mai tsawon fiye da minti 1, Facebook zai saka talla a cikinta. Idan mutum ya kalla wannan tallan, Facebook zai rika tara kudaden bisa adadin masu kallo da tsawon lokacin kallon.
Facebook Reels Ads
Na biyu Reels ads, sune Tallan da suke bayyana a tsakanin ko bayan Reels videos. Wannan sabuwar hanya ce da Meta ta bullo da ita domin masu amfani da Reels su samu kudi. Lokuta da yawa dan kana scrolling zaka ci karo da wadannan tallace-tallacen.
Facebook Stars
Na uku, Facebook stars, shikuma wani tsari ne da yake baiwa masu kallo wato audience dinka damar tura maka “Stars” yayin da kake live ko a yayin da suke kallon videos din ka. Kowanne Star yana kai darajar $0.01.
Sponsored Content
Na hudu, sponsored content, wanda shi ne lokacin da wani brand ko kamfani zasu biya ka domin ka tallata musu kaya ta hanyar dorawa a bidiyoyinka. Irin wannan tsari muna gani sossai daga content creators musamman na kudancin Nigeria.
Affiliate Marketing
Affiliate marketing tsarine da zaka ringa tallata kayayyaki ta hanyar affiliate links. Idan wani ya danna link din ka kuma ya sayi kayan zaka samu commission kai tsaye. Wannan yana da sauki musamman idan ya kasance audience dinka zasu iya sayan kaya, kai tsaye kaje Amazon, ko Selidia kayi register kyauta a matsayin affiliate duk abinda ka gani a wajen kana tunanin za’a saya sai ka kawo shi kayi video a kai. Da zarar an saya to kana da commission.
Abubuwan Da Facebook Ke Bukata Kafin Su Fara Biyanka
Kafin ka fara samun kudi kai tsaye daga Facebook, akwai wasu abubuwa da dole kake bukatar sani kuma ka cike wadannan ka’idoji, sai dai kuma ya danganta ne da kalar monetization din da kake bukata, ga yadda abin yake;
Idan In-Stream Ads ne kana bukatar a Akalla 5,000 followers a Page dinka. Da kuma Akalla 60,000 total watch minutes a cikin watanni 2 da suka wuce, Saboda tabbatar da cewa kana active. Sa’annan kana bukatar a kalla bidiyo 5 wadanda tsawonsu ya kai tsawon (1 min+) a shafin.
Idan kuma Reels Ads ne, kana bukatar Akalla 10,000 followers. Da kuma Akalla 600,000 watch minutes daga videos ko reels dinka.
Yana da kyau ka sani, koda ka cike wadannan sharudan, ba lallai bane ka samu, wato Facebook zasu iya hana ka monetization musamman idan ya kasance contents dinka basu da inganci, misali copyright videos ko kuma abinda yake sabawa dokokinsu, kamar batsa, tashin hankali, zagi, rikicin addini da sauransu.
Kalubalen Da Suke Tattare Da Samun Kudi Daga Facebook
Zaka ci kowa yana maganar Facebook monetization, amma ba kowa bane yake maganar irin kwa-kwar da ake ci ba. Amma maganar gaskiya Facebook yana da tsauri sosai fiye da sauran platforms kamar YouTube da TikTok. Ba wai kawai samun followers da views ba ne bane matsalar ko ma monetization din ba. Ga wasu daga cikin matsalolin da ake fuskanta wanda yawanci bakuda labari:
- Content ID: Idan ka yi amfani da audio ko bidiyo mai copyright, Facebook zasu hanaka monetization.
- Policy Violation: Abu kadan zakayi a Facebook, wasu lokutan ma baka san kayi ba, amma zasu iya hanaka monetization.
- Drop in Reach: Wasu lokutan idan content creator ya rage dora abubuwa masu amfani ko kuma account dinsa ta sauka daga recommendable to algorithm na iya juya masa baya.
- Ad Breaks Bans: Wasu lokuta zaka samu monetization, amma daga baya sai su janye shi ba tare da sunyi maka bayani ba.
Shawara a nan shine, kada kace zaka fara creating na content saboda Facebook monetization kadai, ya kasance kana da wasu missions a kasa.
Yadda Zaka Karbi Kudin Facebook Idan Sun Fara Biyanka
Meta zasu bukaci ka saka bayanan Bank account naka da TIN (Tax ID Number) dinka kafin su biya ka. Haka zalika kana bukatar Meta Payout Account, Banking Details, Sa’annan akwai bukatar ka cika Minimum Threshold na akalla $100 kafin a tura maka kudin.
Ta Yaya Zan Iya Samun Kudi Daga Facebook?
Facebook suna da hanyoyin biya kamar In-Stream Ads, Stars, da Affiliate Marketing. Dole ne ka kirkiro content mai kayatarwa, ka gina followers da views kafin ka fara samun kudi.
Kowane Zai Iya Samun Kudi Daga Facebook?
Ba kowa bane sai iya samun kudin Facebook ba. Sai mutum ya cika wasu sharudda da Facebook suka gindaya kamar yawan followers da mintuna na kallon bidiyo, kuma yanzu Nigeria tana cikin kasashen da ake biya.
Nawa Ne Facebook Suke Biya?
A Facebook kana bukatar ka tara akalla $100 kafin su tura maka kudin. Wannan yana nufin Facebook suna biyan a kalla Naira 150,000 a kudin Nigeria.
Ta Yaya Facebook Ke Biyan Creators?
Facebook yana amfani da bank transfer ko Payoneer. Idan kayi linking da bank account dinka, za’a tura maka kudin kai tsaye bayan ka cika $100.
Posting Kawai Ya Isa Na Ringa Samun Kudi A Facebook?
A’a. Kana bukatar kirkiro engaging content kamar bidiyo, reels, ko live videos. Kuma dole, sai ka cika sharuddan monetization.
Zan Iya Amfani Da Facebook Personal Account Na Samun Kudi?
A’a. Dole ne ka kirkiro Facebook Page ko kuma ka canja profile din zuwa Professional Mode. Wannan shine hanyar da ake amfani da shi wajen samun kudi daga Facebook.
Me Ya Bambanta Facebook Da YouTube Wajen Samun Kudi?
YouTube yana da monetization da ya fi sauki a tracking, amma Facebook yana da karfin virality sosai. Haka kuma, Facebook yana da sabbin models kamar Stars da Paid Subscriptions.
Shin Zan Iya Koyon Facebook Monetization A Simas Academy?
Yes, Simas Academy na da courses masu amfani sosai a bangaren Content Creation da Video Editing wanda zai taimaka maka sossai.