Blog
Yadda Ake Bude Website; Free Blogger Website
- April 6, 2025
- Posted by: Joseph Micheal
- Category: Hausa

A zamanin nan namu samun website yana daga cikin hanyoyin da ke sa mutum ko kasuwanci ya bayyana a idon duniya. Ko kana so ka bude website na kasuwanci, ko shafin koyarwa, to tabbas bude website na iya taimaka maka wajen samun kudi ta internet. Wannan rubutun zai koya maka yadda ake bude website daga farko har karshe, koda kai ba ka da ilimin fasaha.
Menene Website?
Website wani fili ne a internet da mutane ke ziyarta don karanta bayani, duba kayayyaki, ko yin hulda da wani abu, ko saya da sayarwa. Kamar gidan kasuwanci ne amma a kan internet. Yana iya kasancewa shafi guda ne (single page) ko kuma manyan shafuka da dama masu alaka da juna (webpages).
Ire-Iren Websites Da Zaka Iya Budewa
Websites suna da nau’o’i daban-daban bisa ga abin da ake nufi da su. Ga manyan nau’ukan:
- Informational Website – Wannan yana bayar da bayani ne kawai, kamar shafukan gwamnati ko makarantu.
- Business Website – Ana amfani da shi don bayyana kamfanoni da kasuwanci, ana iya nuna ayyukan kamfani da bayanai game da kasuwancin.
- E-Commerce Website – Wannan kalar website din yana bada damar mutane saya da siyarwa ta yanar gizo kai tsaye, kamar Jumia, Selar da Amazon.
- Blog – Shafin rubuce-rubuce ne inda ake wallafa shawarwari, darussa, ko labarai.
- Social Media Website – Ana amfani da su don hulda da sadarwa tsakanin mutane, misali Facebook da Simas Hub.
- Forum Website – Wannan shafi ne don tattaunawa da musayar ra’ayoyi a fannoni daban-daban, misali Nairaland.
- Educational Website – Ana amfani da su wajen koyarwa da ilmantarwa, kamar Flowdiary, Simas Academy, Udemy. Coursera da edX.
- Portfolio Website – Irin wannan website din yana nuna kwarewar mutum kamar mai zane, likita, ko developer.
- News Website – Sune website din da ake posting na sabbin labarai a ciki, kamar BBC Hausa da Daily Trust.
- Entertainment Website – Yana kunshe da nishadi kamar fina-finai, bidiyo da wakoki, misali YouTube da Netflix.
Yadda Ake Bude Website Kyauta
Blogger wata dandalin blog ne da Google ke bayarwa wanda ke bawa kowa damar bude website cikin sauki. Ba sai ka biya hosting ba, kuma da akwai cikakken tsaro da saukin aiki. Wannan yana nufin zaka iya mayar da hankali kan abun da kake rubutawa ba tare da damuwa da wasu abubuwan ba.
Abubuwan Da Kake Bukata Kafin Ka Fara
Kafin ka fara, kana buƙatar:
- Gmail account
- Wani suna da kake so ka sa wa website dinka
- Ra’ayi ko fanni da kake son rubutu ko gabatarwa a kai
Wannan kayan aikin suna da saukin samu, kuma da zarar kana da su, zaka iya fara aikin bude website dinka.
Yadda Ake Bude Blogger Website Cikin Sauki
Da zarar kana da Gmail account, sai ka bi wadannan matakan:
- Ka shiga cikin www.blogger.com tare da Gmail dinka zakayi login.
- Sai ka Danna “Create New Blog”
- Daga nan ka saka sunan blog dinka (title), sannan ka zabi address din da kake so (misali: simasacademy.blogspot.com).
- Danna “Create Blog”, shikenan ka kammala bude website.
Yanzu kana da website naka a Blogger wanda zaka iya fara amfani da shi kai tsaye. Zai kaika ga dashboard dinka inda zaka kalli options da yawa kamar haka.

Yadda Ake Posting A Blogger
Idan kana son fara rubutu a website dinka;

- Danna “New Post” daga dashboard.
- Rubuta title din content dinka a sama.
- A cikin babban filin nan, ka rubuta cikakken labari ko bayani.
- Ana iya saka hotuna ko bidiyo daga icons na dashboard.
- Idan ka gama, danna “Publish” don ya zama public ya haura kan website dinka.
Yadda Ake Gyara Website (Customize)
Blogger yana ba da dama ka gyara yadda website dinka yayi kyau yadda kakeso. Zaka iya:
- Canja launi da fonts daga “Theme” settings.
- Saka menu ko pages irin su Home, Contact Us, da sauransu.
- Gyara layout daga “Layout” tab domin kara gadgets kamar recent posts, archives, ko followers.
Yadda Ake Samun Kudi Daga Website Na Blogger
Daya daga cikin manyan tambayoyi da ake yi shine: “Shin Blogger na bada damar samun kuɗi?” Tabbas! Idan ka gina blog mai inganci, kana iya samun kudi ta hanyoyi kamar:
1. Google AdSense
Wannan shine kamfanin tallace-tallace na Google. Za ka iya connecting na website dinka da AdSense, idan ka samu approval Google zasu dora talla a website din. Idan mutane suna shigowa website din suna kallo ko idan sun danna, za ka sami kudi.
2. Affiliate Marketing
Za ka iya tallata kayan wasu kamfanoni kamar Jumia, Amazon, Selar, SellsRocket, Expertnaire, ValPulse, da sauransu, idan wani ya siya ta dalilinka, zaka sami wani abu daga ciki, maybe 50% ko 30% har 5% ya danganta da yadda ka zaba.
3. Adsterra
Wannan wata ingantacciyar hanyace ta samun kudi daga website wanda a halin yanzu mutane da yawa suna amfani dashi suna samun revenue daga websites dinsu.
4. Sayar Da Kayayyakinka
Idan kana da kaya ko services, zaka iya amfani da Blogger don tallata su kai tsaye ka ringa samun customers.
5. Tallan Mutane (Sponsored Posts)
Idan blog dinka yana samun visitors, za a iya biyan ka domin ka saka tallar wani kuma ka karbi farashin da yayi maka.
Bude website kyauta a Blogger yana da sauki, kuma yana daya daga cikin hanyoyin da za ka iya fara gina gagarumar kasuwanci a intanet. Ko kana son kafa kasuwanci ne, ko koyarwa, ko rubuce-rubuce, Blogger zai baka dama mafi sauki da inganci.