Blog
Yadda Ake Forex Trading (Koyon Kasuwancin Forex)

Kana yawan jin Kalmar ‘Forex’ amma watakila baka santa ba? Yau zaka fahimci yadda ake Forex Trading. Da farko Kasuwancin Forex, wanda ake kira da Foreign Exchange, hanya ce da mutane ke amfani da ita wajen samun kudi a online cikin sauki ta hanyar saya da sayarwa. A saukake, ana amfani da darajar manyan kudaden duniya domin a saya a lokacin da suka fadi, sannan a sayar idan suka karu. Forex Trading (FX) tana daya daga cikin kasuwancin mafi girma a duniya, domin ana canja (Exchange) fiye da dala tiriliyan 6 ($6 Triillion) kullum.
Amma fa, kafin mutum ya shiga wannan harkar, yana da matukar muhimmanci ya fahimci yadda kasuwar take aiki, menene hadarinta, da kuma yadda zaka kiyaye kanka daga asarar kudade. Wannan article din zai koya maka komai daga tushe har zuwa matakin nasara kan yadda ake Forex trading, ko da kuwa ba ka da kwarewa. Muje zuwa…
Menene Forex Trading?

Forex Trading na nufin ciniki da kudaden kasashe daban-daban, kamar naira da dala, ko euro da yen, dala da euro, ko dala da gold. Ana yin haka ne duka ta hanyar amfani da internet, inda mutane da kamfanoni ke saya da sayarwa a lokaci daya.
Misali, idan ka shiga kasuwar dala da euro (EURUSD), kuma kana ganin cewa darajar Dala zata karu a kan Euro, zaka iya sayen Dala da Euro, sannan idan Dalan ya karu, sai ka sayar (TP) don samun riba. Wannan shine asalin tushen Forex trading.
Abubuwan Da Kake Bukata Don Fara Forex Trading
Idan kana son fara kasuwancin Forex trading, ba dole sai ka bude office ko ka dauki ma’aikata ba. Wannan wayar dake hannunka, data da kuma kuma sanin wasu abubuwa. Ga abubuwan da kake bukata:
Ilimi
Dole kana bukatar ilimin Forex kafin ka shiga, Ba zaka iya farawa ba har sai ka samu cikakken iliminta tare da horo (maybe daga mentor/malaminka, ko academy da kake koya). Sa’annan kar kayi gaggawa, ka fara fahimtar kasuwa da strategies da zakayi aiki dasu shine sirrin nasara a harkar Forex.
Broker
Kana bukatar kayi register da broker da zaka iya aiki da ita cikin sauki. Muna da brokers da yawa, amma wasu suna da features din da babu a wasu, zaka iya bincike a kan wannan kafin ka yanke hukuncin wanda zakayi aiki dashi, watakila daga academy din da kake ko kuma mentor din ka ya samar maka. Wasu daga cikin brokers sun hada da Exness, OctaFX, XM, IC Markets da sauransu.
Trading Platform
Yawanci brokers suna bada damar amfani da MetaTrader 4 (MT4) ko MetaTrader 5 (MT5) domin yin trading. Yin amfani da MT5 ko MT4 zai baka damar kayi running na trading dinka cikin sauki.
Capital
Dole kana bukatar jari idan kana son fara kasuwancin Forex. Kuma zaka iya farawa da $10 zuwa $100 ko sama da hakan idan da hali, amma yana da kyau ka fara da demo account kafin saka asalin kudi. Wasu zaka samu suna daukar sama da shekara suna amfani da demo suna ta practice kafin nan su saka asalin kudin su. (Forex harka ce ta masu hakuri da juriya gaskiya).
Baya ga haka, kana bukatar ka koyi yadda tsarin tattalin arziki yake tafiya (fundamental analysis) da kuma yadda mutane suke juya kasuwar (technical analysis). Duk wannan suna daga cikin ilimin da zaka koya daga Forex.
Matsalolin Forex Da Yadda Ake Kauce Musu
Duk da cewa Forex trading na kawo riba, amma sai dai akwai hadarurruka masu yawa da ke tattare da shi. Abu na farko da ya kamata ka sani shi ne: mutanen da ke asara a Forex sun fi yawa fiye da wadanda suke samun riba. Wannan na faruwa ne saboda mutane da dama suna shiga harkar ba tare da cikakken ilimi ko strategies da suka dace ba.
Wasu daga cikin Matsalolin Forex:
- Rashin Sarrafa Yanayinka (Emotion) – Idan kana Jin tsoro ko kana cikin farin ciki sosai yana iya sa ka yanke shawara mara kyau.
- Amfani Da Leverage Da Yawa – Leverage yana iya sa ka samu riba sosai a kowane trade, amma yana iya kuma sa ka rasa komai a lokaci daya.
- Rashin Tsari Da Strategy – Idan baka da tsarin shiga kasuwa (trading strategy), zai yi wuya ka ci gaba da samun riba. Duk wadanda kaga sunyi nasara a harkar Forex to zaka samu suna da strategy da suke amfani dashi kuma basu tsallakawa.
Don haka yana da kyau ka fahimta sosai, kayi ka fara gwaji da demo account, sa’annan ka dinga koyo daga kwararrun traders (so samu ka nemi mentor) kafin nan ka shiga kasuwa da kudinka.
Karanta: Sirrin Crypto: Yadda Ake Kasuwancin Cryptocurrency.
Menene Leverage A Forex?
Leverage wata hanya ce da broker ke bawa traders damar yin trading da kudi fiye da wanda yake dashi a asusunsa. Misali, leverage na 1:100 yana nufin idan kana da $10, zaka iya trade na $1,000 a kasuwa. Wannan yana nufin kana iya samun riba mai yawa da kudi kalilan, amma kuma hadarinta ya fi yawa.
Saboda haka Kada ka bari leverage ya rude ka. Ka fara da leverage kadan kamar 1:10 ko 1:20, sannan ka ringa karawa da hankali idan kana samun kwarewa.
Me Yasa Yawancin Mutane Ke Asara A Forex?
Akwai dalilai da dama da yasa yawancin sabbin shiga harkar Forex ke asara. Ga wasu daga ciki:
- Rashin karatu kafin su shiga
- Gaggawa da rashin hakuri
- Suna Dogaro da shawarwarin mutane maimakon koyaon nasu
- Trading da emotions (zuciya) maimakon gina strategy
- Rashin amfani da stop loss da take profit
Shawari
Kasuwancin Forex babbar dama ce da ke iya kawo riba sosai idan aka bi hanya mai kyau. Amma yana bukatar horo, ilimi, da tsari. Kada ka gaggauta sa kudinka a kasuwa tun farko, ka fara da demo trading kuma ka koyi yadda abubuwa ke aiki. Ka koyar da zuciyarka da sarrafa kai kafin ka sarrafa kasuwa.
FAQs – Yadda Ake Forex Trading
Menene Forex Trading?
Forex Trading Shi Ne Kasuwancin Sauya Kudi Tsakanin Kasashe Don Samun Riba.
Shin Forex Trading Halal Ne Ko Haram?
Dangane Da Fahimtar Malamai, Halaccin Forex Na Dogara Ne Da Kalar Trading Da Ka Ke Yi. Amma Da Yawa Daga Cikin Malamai Suna Cewa Idan Dai Akwai Marging To Ya Zama Haram. Yana Da Kyau Kayi Bincike Kafin Ka Fara.
Ta Yaya Zan Fara Forex Trading?
Zaka Iya Farawa Da Bude Demo Account, Karanta Koyarwar Forex, Sannan Ka Fara Trading Da Kadan-Kadan.
Zai Yiwu In Samu Kudi A Forex?
Kwarai Zai Yiwu, Da Akwai Matasa Da Yawa Da Sukayi Arziki Ta Forex. Amma Ba Lokaci Daya Ba, Yana Bukatar Ilimi, Hakuri, Da Dabaru.
Wane Leverage Yafi Daidai Ga Masu Farawa?
Leverage Na 1:10 Zuwa 1:20 Yafi Ga Wadanda Zasu Fara Domin Risk Management.
Menene Stop Loss Da Take Profit A Forex?
Stop Loss Tsarin Kariya Ne Da Ake Saitawa Daga Yin Asara, Yayin Da Take Profit Kuma Yake Taimakawa Wajen Samun Riba Lokacin Da Farashi Ya Kai Matakin Da Ka Ke So.
Idan kana da wata tambaya kai tsaye game da Forex Trading zaka iya yi ta comment dake kasa.
Message *pls i need ur whatsapp no pls
mene farkon app a ina zakasa shi