Blog
Sirrin Crypto: Yadda Ake Kasuwancin Cryptocurrency
- April 6, 2025
- Posted by: Joseph Micheal
- Category: Hausa Cryptocurrency

Watakila kana yawan jin kalmar cryptocurrency amma baka fahimta ba? Ko kana son ka fara kasuwancin crypto amma baka da ilimi ko kwarewa? Wannan posting din zai taimaka maka wajen fahimtar Menene Crypto daga A to Z, da bayani dalla-dalla da za ka iya bi. A wannan post din, za mu warware duk abubuwan da suka shafi cryptocurrency, daga menene shi, har zuwa yadda zaka iya saya, ajiya, da kasuwanci da shi cikin sauki ka samu riba.
Menene Cryptocurrency?
Cryptocurrency wani nau’in kudi ne na zamani da ake amfani da ita a yanar gizo. Ba kamar kudin da muke rikewa a hannu bane, crypto ba ta da takarda ko tsabar kudi (coin), tana amfani ne da wasu codes da fasahar blockchain wanda yake samar da tsaro da inganci.
Misalan Cryptocurrency (Coins/Tokens)
Wasu daga cikin Cryptocurrencies sun hada da Core, Pi, BNB, Solana, USDT, da XRP, TON. Amma da akwai sauran kudaden da ake trading dasu da yawa, Bitcoin (BTC) Shi ne na farko kuma mafi shahara, sai kuma Ethereum (ETH).
Yaya Cryptocurrency Ke Aiki?
Cryptocurrency tana aiki ne ta fasahar blockchain, wanda wata hanya ce da ke recording din duk wani trade din da ake yi. Sa’annan kuma bata karkashin ikon sarrafawar wata gwamnati ko banki.
Kowane lokaci idan wani ya tura ko an tura nasa crypto, ana recording din transaction din ne a cikin wani babban kundin bayanan (blockchain), wanda ke bayyana gaskiyar abin da ya faru ba tare da boye-boye ba. Kowa zai iya tracking na account (wallet) ya kalli abinda yake ciki da transactions da akayi.
Yadda Ake Fara Kasuwancin Cryptocurrency
Mataki 1: Kirkirar Wallet
Wallet shine account na ajiyar kudin crypto. Kamar asusun banki ne na crypto. Muna da wallet kala biyu:
- Hot Wallet: Ana amfani dashi da internet, misali kamar Trust Wallet, TonKeeper, MetaMask, da Binance Wallet.
- Cold Wallet: Ba ya amfani da internet (online) – kamar Ledger ko Trezor, ana haka ne don karin tsaron crypto daga barayi.
Mataki 2: Bude Exchanger
Wannan shine inda zaka ringa saya ko sayar da crypto. Exchanger mafi sauki da amfani sune: Binance (Shine mafi girma a duniya), Paxful/Yellow Card (Da shi zaka iya siyan crypto da Naira), KuCoin, Bybit, Bitget, MEXC, da Coinbase da sauran platforms.
Mataki 3: Yin KYC
Yawancin exchange suna bukatar kayi KYC, inda zaka Dauki hoton fuskarka don tabbatar da cewa kai ne. Bayan nan ka tura hoton ID dinka (kamar katin dan kasa ko driving license).
Mataki 4: Sayan Crypto
Idan ka zo wannan matakin yanzu zaka iya Siyan crypto ta hanyar banki ko USDT. Zaka zabi crypto da kake so ka saya, kamar Bitcoin, Ethereum, ko BNB. Sa’annan ka tura a wallet dinka.
Yadda Ake Kasuwanci (Trading) Da Crypto
Kasuwanci yana nufin siye lokacin farashi ya yi kasa, da sayarwa lokacin farashin ya tashi.
Two Types Of Trading:
- Spot Trading: Siye da sayar da crypto nan take, kamar siyan kaya a kasuwa lokacin da suka fadi, a sayar lokacin da suka tashi.
- Futures Trading: Kamar caca ce akan farashin crypto zai hau ko zai sauka, kana bukatar ilimi sossai kafin ka shiga wannan saboda yana da hatsari sossai.
Abubuwan Da Zaka Kula Da Su A Harkar Trading
- Technical Analysis: Inda zaka nazarci yadda kasuwa take.
- Fundamental Analysis: Nazarin labarai da abubuwan da ke tasiri ga crypto.
- Risk Management: Ka kula da wannan, kada ka ringa shiga kasuwa da kudadenka gabadaya once, ka raba su kashi-kashi.
Karanta: Yadda Ake Forex Trading (Koyon Kasuwanci Forex).
Hanyoyin Samun Kudi Da Crypto
Harkar crypto ba iya trading bane kawai, ko kuma ka sayi coins/tokens/NFT ka ajiye ba. Ga wasu hanyoyin da zaka samu kudi ta crypto dasu:
- Trading (Siya da Sayarwa): Shine aka fi yi a Crypto.
- Airdrops: Samun crypto kyauta daga projects (musamman ma sabbin projects).
- Staking: Zuba crypto don samun karin crypto kyauta.
- Mining: Aiki da kwamfuta, yana bukatar computers sossai da office na musamman.
- NFTs: Zanen dijital da ake siye da crypto, zaka iya zanawa ka mayar NFT (minting).
Kalubale Da Hadurran Kasuwancin Crypto
- Canjin Farashi: Yana iya tashi ko faduwa cikin lokaci kadan ta yadda zaka iya yin asara mai yawa kafin ka ankara.
- Zamba (Scams): Ana yawan samun scammers a harkar. Ka gujewa shiga wuraren da baka yarda da su ba.
- Rashin Sanin Hanya: Yana da kyau ka koya sosai kafin saka jari. Muna da influencers na Hausa a duniya harkar crypto, zaka iya binsu a social media kana koya daga garesu.
Karanta: Yadda Ake Samun Kudi A Online.
Shawarwari Ga Masu Farawa
- Ka fara da karamar jari.
- Kada ka ringa bin abinda mutane suke cewa haka kurum a social media kamar bada signal ko shawara, musamman yan gama gari, DYOR.
- Ka ringa amfani da demo account kafin fara trading da asalin kudinka.
- Ka nemi mentor ko ka shiga class da zaka koyi karatu. Ko ka koya daga online schools irinsu Flowdiary, Simas Academy, Binance Academy, ko YouTube (SCTv Africa).
Cryptocurrency sabuwar hanya ce da mutane ke amfani da ita don samun ‘yanci na kudi da damar yin kasuwanci. Amma kamar kowanne fanni, shima harkar crypto yana bukatar ilimi, tsari, da juriya. Kada ka gaggara, ka koya yadda kasuwar ke tafiya, ka ringa bibiyan mutanen cikinta hausawa da turawa kana koyon yadda abin yake, kuma kana gwadawa.
FAQs
Menene Cryptocurrency Kuma Ta Yaya Take Aiki?
Cryptocurrency wata kudi ce ta zamani da ake amfani da ita a yanar gizo. Tana aiki ne ta hanyar fasahar blockchain ba tare da gwamnati ko banki sun shiga ciki ba.
Ta Yaya Zan Iya Fara Kasuwancin Crypto?
Zaka fara ne ta hanyar mallakar wallet, sa’annan kayi rijista da exchange, da siyan crypto da kake so kamar Bitcoin ko Ethereum.
Wani Nau’in Wallet Yafi Ga Masu Farawa?
Masu farawa zasu iya amfani da hot wallet kamar Trust Wallet, Metamask ko Binance Wallet domin saukin amfani.
Shin Zai Yiwu Na Samu Riba Daga Crypto?
Sossai ma kuwa, amma kana bukatar fahimta da ilimi sosai. Farashin crypto na iya tashi ko sauka, don haka akwai damar riba da faduwa.
Menene Bambanci Tsakanin Spot Da Futures Trading?
Spot trading na nufin mallakar crypto da gaske, yayin da futures trading kuma caca ne akan farashin crypto zai hau ko ya sauka.
Ina Zan Koyi Crypto Da Hausa?
A Simas Academy da akwai courses dake bayar da cikakken ilimi kan crypto da kasuwanci a cikin harshen Hausa, wanda ya dace da masu farawa da kuma masu matsakaicin kwarewa.
[…] Karanta: Sirrin Crypto: Yadda Ake Kasuwancin Cryptocurrency. […]