Blog
Yadda Ake Samun Kudi A YouTube; Koyon Bude Channel
- April 7, 2025
- Posted by: Joseph Micheal
- Category: Hausa

YouTube na daya daga cikin kafofin da mutane da dama ke amfani da shi wajen samun kudi daga internet, ta hanyar creating na bidiyoyi masu amfani ko nishadi. Ko da kuwa ba ka da kawarewa ko kayan aiki na musamman, za ka iya fara kasuwancin ka samu kudi a YouTube cikin sauki. Wannan rubutun munyi bayani zai yadda ake bude youtube channel daga farko har a fara biyan ka.
Yaya Tsarin Samun Kudi A YouTube Yake
Monetization a YouTube yana nufin samun kudi daga videos dinka. Ana biyan kudin ne ta hanyoyi da dama kamar AdSense, sponsorships, super chat, da kuma affiliate marketing. Amma kafin ka fara samun kudi, akwai wasu sharudda da YouTube ke bukata.
Abubuwan Da Ake Bukata Kafin Fara Samun Kudi A YouTube
Kafin ka fara samun kudi a YouTube, dole ne ka hada wadannan abubuwan:
- Samun subscribers 1,000+.
- Ka Samu awanni 4,000 na kallo wato watch time hours a tsakanin shekara guda.
- Dole Kayi linking channel dinka da AdSense account.
- Ka bi dokokin YouTube, musamman Community Guidelines da kuma Copyright rules, domin YouTube basu wasa da wannan bangaren.
Idan ka cika wadannan sharuddan, za ka iya shiga tsarin YouTube Partner Program (YPP) kaima ka fara samun kudi a YouTube.
Yadda Ake Bude Channel Na YouTube

Bude channel a YouTube abu ne mai sauki:
- Ka bude Google account (Gmail) idan baka da shi.
- Sai Ka shiga YouTube.
- Zaka ga hoton profile (a sama gefenhagu) ka danna ka zabi “Create a Channel”.
- A nan zaka saka sunan da ka ke so, hoton channel, username, da description dinsa.
- Daga nan zaka iya fara dora videos dinka.
Zabar Niche Da Zaka Mayar Da Hankali
Yana da kyau ka zabi niche, waro fannin daya da zaka mayar da hankali a kai. Wannan zai taimaka wajen jawo masu kallo oraganic (na gaske). Ga wasu daga cikin fannoni da suka fi samun kallo a Najeriya da duniya:
- Nishadi (Comedy)
- Ilimi (Tutorials, Karatu)
- Business (Kasuwanci, Nasiha)
- Kayan Abinci (Girke-girke)
- Fasaha da Kere-kere
- Wakoki
Ana samun millions of Naira daga YouTube a yanzu, idan kana da idea a kan abinda zakayi kar ka tsaya wasa da damarka.
Yadda Ake KirKirar Bidiyo
Ko da ba ka da kyamara mai tsada, zaka iya fara amfani da wayarka ta android kamar yadda yawanci YouTubers suke yi. Muhimman abubuwan da kake bukata sun hada da:
- Hoton bidiyo mai kyau (HD)
- Sound mai kyau (kar a ji hayaniya ko low voice)
- Editing app mai kyau kamar CapCut, Kinemaster, VN, ko Filmora.
- Thumbnail mai jan hankali domin jawo hankalin masu kallo su danna.
Abu mai sauki, zaka iya koyon video editing da Hausa a Simas Academy ko Flowdiary, zaka iya zuwa a koya maka cikin sauki.
SEO A YouTube
Kamar Google, YouTube yana amfani da SEO (Search Engine Optimization). Wannan yana nufin:
- Rubuta title mai jan hankali.
- Saka keywords da mutane ke searching.
- Yin amfani da description da tags da suka dace da videos dinka.
- Kirkirar thumbnail da zai ja hankalin viewers.
Misali, idan kana koyar da “Yadda Ake Girki”, title dinka zai iya zama: “Yadda Ake Dafa Tuwo Mai Dadi – Hausa Recipe”. Da sauransu. Idan kana da ra’ayin koyon SEO course da akwai shi a Simas Academy, yadda zaka ringa samun customers daga wajen searching, ko TikTok, YouTube, Facebook, da website dinka.
Hanyoyin Samun Kudi A YouTube
Bayan ka cika sharuddan da muka ambata a baya na YPP, za ka fara samun kudi daga hanyoyi da dama:
1. Google AdSense
Ana saka tallace-tallace wato Ads a cikin vdieos dinka (ka lura idan kaje kallin videos a YouTube), kuma idan mutane suka kalla ko suka danna tallan, zaka samu kudi daga YouTube.
2. Sponsorship
Kamfanoni za su biya ka don ka ringa ambatar kayansu ko ka tallata su a cikin videos dinka kana samun kudi.
3. Super Chat & Membership
Masoyanka za su iya aiko maka da kudi kai tsaye yayin live stream ko su shiga membership plan dinka na musamman. Kamar dai yadda ake yi a TikTok.
4. Affiliate Marketing
Za ka iya tallata kayayyakin wasu kuma a baka kaso idan mutane sun sayi su ta hanyar link dinka. Wanna shine hanyar da YouTubers da yawa suke amfani dashi musamman wadanda Google AdSense basu karbesu ba.
5. Sayar Da Kayayyaki
Idan kana da hajarka kamar riguna, littattafai, ko kayan zamani, zaka iya tallata su a channel dinka. Amma ka tabbatar niche dinka ya dace da kayayyakin da kake sayarwa.
Shawarwari Ga Masu Farawa
- Ka kasance kana da tsari: Publishing na vdieos akai-akai (misali sau daya ko sau biyu a sati).
- Ka ringa bin comments: Ka ringa reply don kara gina alakarka da masu kallonka.
- Cigaba da koyo: Ka ringa duba yadda shahararrun YouTubers ke yin bidiyonsu.
- Kar kace zaka daina – YouTube yana bukatar hakuri da juriya sossai, saboda haka kana bukatar maximum juriya.
Daga karshe, YouTube platform ne da ya kasance hanyar samun arxikin mutane da yawa, musamman wadanda sukayi hakuri dashi. Idan dai kana da wayar hannu kuma kana da sha’awar yin YouTube zaka iya fara gina channel din da zai kawo maka kudi. Kada ka jira sai ka zama kwararre, zaka iya farawa fara yanzu, zaka zama gwani idan kaci gaba.
Idan kana da tambaya ko kana son karin bayani, zaka rubuta mana a comment ko kayi mana ta Simas Academy idan kana son koyon YouTube business.
Yaya Zan Fara Samun Kudi A YouTube Channel Dina?
Domin fara samun kuɗi a YouTube, dole ne ka samu akalla subscribers 1,000 da kuma 4,000 watch time hours a cikin shekara guda, sannan ka hada channel dinka da AdSense ta cikin YouTube Studio.
Yaya YouTube Suke Biyan Mutane?
Ana biyan YouTubers ne bayan sun tara abinda ya kai $100 a cikin AdSense account dinsu, sannan ana biyansu kowane wata, yawanci ranar 21 zuwa 26.
Za A Iya Samun Kuɗi Ba Tare Da Cika 4,000 Watch Hours Ba?
A’a, idan kana son fara samun kudi daga YouTube ta hanyar AdSense, dole ne ka cika 4,000 watch hours da 1,000 subscribers. Amma akwai wasu hanyoyi kamar affiliate marketing da sponsorship da zaka iya farawa da su tun kafin ka cika sharuddan YouTube.