Have a question?
Message sent Close

Basic Digital Literacy

Basic Digital Literacy Course Simas Academy
Instructor
Joseph Micheal
0
0 reviews
  • Description
  • Curriculum
  • FAQ
  • Reviews

Wannan Course Din Zai Koyar Da Kai Yadda Zaka Fahimci Duniyar Digital Da Sirrinta, Daga Mataki Na Farko Har Zuwa Matakin Da Zaka Iya Amfani Da Wayarka Ko Laptop Naka Domin Neman Ilimi, Ayyuka, Da Damar Samun Kudi Kai Tsaye Daga Ko Ina.

Za Ka Fahimci Yadda Duniya Ta Canza Daga Analog Zuwa Digital, Abubuwan Da Ba Kowa Ya Taba Faɗa Maka Ba Game Da Intanet, Da Yadda Za Ka Yi Amfani Da Zubin Fasaha Don Gina Kanka A Zamanance

An Tsara Wannan Course Ne Cikin Harshen Hausa Kai Tsaye, Babu Kalamai Masu Nauyi Da Zasu Baka Wahalar Fahimta. Ko Kai Matashi Ne Da Bai San Komai Game Da Intanet Ba, Ko Mace Ce Dake Gida Da Ke Neman Ilimi Don Shiga Harkar Internet, Wannan Course Zai Bude Maka Idanu Ka Fahimci Abubuwan Da Zasu Canza Rayuwarka, In Sha Allahu.

🧠 Me Za Ka Koya A Wannan Course Din?

  • Menene Digital World, Da Yadda Ta Sauya Rayuwarmu

  • Sirrin Amfani Da Wayarka Wajen Koyon Ilimi Da Nemawa Kai Mafita.

  • Yadda Ake Yin Amfani Da Internet Don Samun Ilimi Da Bayanai

  • Yadda Za Ka Kirkiri Accounts Da Amfani Da Google Drive, Docs, Words, Da Sheets

  • Yadda Ake Karatun A Makarantun Online Kamar Udemy, Coursera, Simas Academy, Malamiromba

  • Muhimmancin Tsare Sirri A Intanet Da Kare Kanka Daga Matsaloli

  • Yadda Zaka Yi Amfani Da WhatsApp Business, Zoom, Da Sauran Kayan Aiki

  • Canza Tunaninka Domin Amfani Da Intanet Ta Hanya Mai Kyau

  • Gano Scammers, Ponzi Schemes, Get Rich Quick Shemes Da Sauransu

  • Yadda Zaka Shirya Rayuwarka Ta Digital Don Gaba

💡 Wannan Course Din Zai Taimakawa:

  • Matasa Masu Sha’awar Ilimi Na Zamani Da Internet

  • Matan Gida Masu Sha’awar Shiga Harkar Internet

  • Dalibai Da Ke Da Wayar Hannu Ko Computer

  • Mutanen Da Suke So Su Canza Rayuwarsu Ta Hanyar Intanet

A Nan Ba Iya Digital Literacy Zaka Koya Ba, Wannan Shi Ne Tushen Ilimin Duniyar Intanet Gabadaya.

Mene Ne Digital Literacy Course?
Digital Literacy Course Ilimi Ne Na Musamman A Shake Waje Daya Da Zai Koya Maka Muhimman Ilimin Fasaha Da Internet Domin Ka Iya Amfani Da Wayaka Ko Laptop Don Kasancewa A Duniyar Internet.
Me Zaka Koya A Wannan Course Din?
Zaka Koyi Abubuwa Da Yawa, Kama Daga Fahimtar Yanar Gizo, Tsaron Kai, Kula Da Bayanai, Sayan Kaya, Gano Karya Da Gaskiya, Scams, Fake, Da Sauransu. Abubuwa Da Yawa.
Shin Wannan Course Din Zai Nuna Mini Yadda Zan Yi Aiki Online?
Kwarai Ma Kuwa, Wannan Course Din Zai Bude Maka Idanu Da Fahimtar Ayyukan Online, Ba Neman Kudi Kai Tsaye Ba! Zai Taimaka Maka Wajen Koyon Kowane Skill Online Da Kuma Yin Abubuwa A Ilimance.
Mene Ne Muhimmancin Wannan Course Din?
100% Wannan Course Din Zai Taimaka Maka Wajen Fita Daga Jahilcin Fasaha, Ka Koyi Amfani Da Intanet. Wannan Foundation Ne Na Rayuwar Internet Da Dole Kana Bukatar Ka Sani.
Shin Wannan Course Din Yana Bukatar Saka Kudi A Internet?
A'a Babu Baka Bukatar Wannan.
Wa Zai Amfana Da Wannan Course Din?
Kowa Da Kowa Da Ke Da Wayar Hannu Ko Laptop Zai Iya Amfana Muddin Yana Da Sha'awar Shiga Harkar Internet, Ko Matashi Ne, Ko Dalibi, Ko Mace Da Ke Gida, Ko Wanda Ke Neman Ilimin Domin Bunkasa Kansa.
Shin Wannan Course Din Zai Iya Taimakawa Wajen Samun Kudi?
Zai Taimaka Maka Ka Fahimci Hanyoyin Samun Kudi Ta Intanet, Ta Hanyar Ilimi Da Kwarewa, Saboda Digital Skills Sune Abinda Duniya Ke Bukata Yanzu.