- Description
- Curriculum
- FAQ
- Reviews
Wannan Course Din Zai Koya Maka Yadda Zaka Shiga Duniyar Social Media Content Creation Ko Kuma Digital Journalism Da Cikakken Iliminta.
Zaka Fahimci Komai Daga 0% Farko Har Zuwa Matakin Da Zaka Iya Rubuta Labarai, Yin Editing, Samar Musu Da Inganci, Da Kuma Amfani Da Kayan Aikin Zamani.
Za Ka Fahimci Yadda Kafofin Labarai Suka Canza Daga Gidajen Redio Da Jaridu Zuwa Shafukan Yanar Gizo Da Social Media, Da Yadda Kai Ma Zaka Iya Bibiyar Wannan Sauyi, Ka Zama Muryar Al’umma Ba Tare Da Jahilci Ba.
An Tsara Wannan Course Ne Cikin Hausa Kai Tsaye, Babu Wasu Complicated Words, (Kalamai Masu Nauyi) Da Zasu Baka Wahalar Fahimta. Koda Kai Din Mai Ra’ayin Shiga Harkar Jarida Ne, Ko Dalibi, Ko Ma Wani Da Ke Son Gina Sunansa A Social Media Da Internet, Wannan Course Zai Bude Maka Hanya Ka Fahimci Abubuwan Da Zasu Sauya Maka Tafiya.
Abubuwan Da Zaka Koya A Wanna Program Din.
-
Menene Digital Journalism Da Muhimmancinsa
-
Yadda Ake Rubuta Labarai Masu Inganci Da Daɗi Ga Masu Karatu
- Yadda Ake Hira Da Mutum, Da Kuma Samo Labarai
-
Hanyoyin Ganowa Da Gujewa Fake News
-
Editing Na Video, Hotuna Da Rubutu Domin Inganta Ayyuka
-
Amfani Da Blogging Platforms (Publishers)
-
Amfani Da Social Media Wajen Yada Labarai Da Gina Audience
-
Tsaron Bayanai Da Kare Kai A Matsayin Dan Jarida
-
Yadda Zaka Yi Amfani Da AI Wajen Rubutu, Bincike Da Tsara Ayyuka
-
Hanyoyin Neman Aiki, Samun Kuɗi, Da Gina Suna
Wannan Course Din Zai Taimaka Wa:
-
Matasa Masu Son Zama ’Yan Jaridan Zamani Ko Karin Ilimi
-
Wadanda Ke Son Kwarewa Da Samun Damar Ayyuka (Jobs)
-
Masu Sha’awar Rubutu, Blogging, Da Gina Sunansu A Online
- Yan Kasuwa Da Matasa Da Suke Son Kirkiro News Media Agency
-
Matan Gida Ko Ma’aikata Da Ke Son Kara Iliminsu Wajen Aiki Ko Samun Abin Yi
A Wannan Darasin Ba Kawai Journalism Din Zaka Koya Ba, Hatta Blogging Basic, AI, Publishing, Self-Protection, Tabbatar Da Ingancin Labarai, Samun Damar Aiki A Kowane Bangare Da Sauransu. Kar Ayi Banda Kai.